Uncategorized

Allah Ya Yi Rasuwa Wa Gogaggen Dan Jarida, Shehu Saulawa

Daga Khalid Idris Doya

Allah ya yi rasuwa wa gogaggen dan jarida nan, Malam Shehu Saulawa na gidan redoyon Radio France International (RFI) rasuwa.

Ya rasu yana da shekara 63 a duniya, kuma ya bar mata guda daya da ‘ya’ya 5; – maza 2, mata 3.

Saulawa ya rasu ne a jiya Litinin bayan shafe sama da shekara daya yana fama da jinya. An yi masa jana’iza ne a masallacin Juma’a na Gwallaga da ke cikin garin Bauchi a ranar Talata.

Shi dai Shehu Saulawa dan asalin jihar Katsina ne ya yi aikin jarida a kamfanin dillacin labarai ta kasa (NAN) daga bisani ya koma gidan rediyon BBC Hausa bayan barin BBC kuma har zuwa lokacin rasuwarsa yana aiki da gidan rediyon RFI.

Kazalika, yana koyarwa a tsangayar koyar da aikin jarida a kwalejin kimiyya, fasaha da kere-kere mallakin gwamnatin jihar Bauchi (ATAP) kafin rasuwarsa.

Da ya ke mika sakon ta’aziyyar abokan aikinsa a gidan mamacin, Malam Ahmed Muhammad, shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai a jihar Bauchi, ya misalta marigayin a matsayin dattijon kwarai, mai hakuri, son zaman lafiya, iya mu’amala da kowa.

Kana ya kuma kara da cewa, tsawon lokacin da suka yi aiki tare da marigayin, sun shaide shi da nuna gaskiya rikon amana kuma ya kasance mai bin ka’ida da dokokin aiki a kowani lokaci.

Don haka, Ahmed ya misalta rasuwar Shehu Saulawa a matsayin babban rashi ga ‘yan jarida a fadin kasar nan, ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa ya kuma sanya shi cikin aljanna madaukakiya.

Wakilinmu ya nakalto cewa, ‘yan jarida da dama ne suka nuna jimami da alhinin rasuwar Saulawa, inda suka yi dafifi wajen jana’izarsa tare da masa rakiya zuwa makabarta.

Leave a Reply