Uncategorized

An Ga Jaririn Watan Ramadana A Saudiyya

Daga Muhammad Kaka Misau

Hukumomi a kasa mai tsarki ta Saudiyya sun sanar da cewa, an samu ganin jaririn watan ramadana a yankuna da dama, don haka gobe Asabar ne zai kasance ranar daya ga watan Ramadana.

Kafofi daga kasar Saudiyya sun tabbatar da hakan, inda tunin al’ummar Musulmai suka fara shirye-shiryen daukan Azumin watan Ramadana a goben.

Allah ya sa a fara a sa’a a kammala a sa’a, kuma muna fatan Allah amshi ibadodinmu.

Leave a Reply