Hausa

APC Ta Lashe Dukkanin Zaben Shugabannin Kananan Hukumomin Gombe

Daga Khalid Idris Doya

Jam’iyyar APC da ke mulki a jihar Gombe ta lashe dukkanin zaben shugabannin kananan hukumomin jihar baki daya.

LEADERSHIP ta labarto cewa jam’iyyu 5 ne suka shiga aka fafata neman sa’a a zaben kananan hukumomi 11 na jihar da ya gudana a ranar Asabar, jam’iyyun sun hada da APC, PDP, YPP, Accord Party da Zenith Labour Party (ZLP).

Babban jami’in tattara sakamakon zaben kuma shugaban hukumar shirya zabe ta jihar Gombe (GOSIEC), Sa’idu Awak, shi ne ya sanar da sakamakon zaben, bugu da kari a cewarsa APC din ta kuma lashe dukkanin zabukan kansiloli ba tare da hamayya ba a gundumomi 114 da suke fadin kananan hukumomi 11 na jihar.

Da ya ke jero yadda zaben ya gudana, Awak ya ce a karamar hukumar Gombe dan takarar APC Sani Haruna shi ne ya lashe zaben da kuri’a 72,286 inda ya kayar da abokin tarakarsa na PDP da ya samu kuri’u 1,678. Sannan, a karamar hukumar Kwami Ahmed Doho ne ya lashe da 29,073 inda ya lasa abokin nemansa na PDP mai kuri’u 1,930.

Balanga: Ibrahim Salisu da kuri’ 35,493 yayin da na PDP ya sa mu kuri’u 184 kacal. Sai Billiri Egla Idris na APC mai nasara da kuri’u 33,979 gami da kayar da dan takarar PDP mai samun kuri’a 2,088.

A karamar hukumar Akko kuwa nan ma dai APC ce ta lashe inda mai rike mata tuta Mohammed Adamu ya samu 65,066 a kan na PDP mai kuri’a 3,058. Karamar hukumar Funakaye ma, Shuaibu Abdulrahman na APC ne ya zama shugaban karamar hukumar da kuri’a 36,026 inda ya maka na PDP a kasa da ya samu kuri’u 3,094.

Karamar hukumar Yamaltu-Deba ma dai, dan takarar APC Abubakar Difa aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 57,546 inda ya kayar da abokin nemansa na PDP da ya sami 1,334. A Dukku, APC – Adamu Waziri ya samu 26,869 da kayar da na PPP 4,821.

Shugaban hukumar zaben ya kuma ce a karamar hukumar Nafada, dan takarar APC, Babagida Adamu ne ya lashe zaben da kuri’u 17,977 da ya kawar da na PDP mai kuri’a 355 kacal.

Bugu da kari, a karamar hukumar Kaltungo da Shongom ‘yan takarar APC Iliya Suleiman Jatali da Binta Bello, ne suka lashe zabukan ba hamayya.

Leave a Reply