HausaLatest

‘Ayyukan ta’addanci na karuwa a Kano’

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje

Tabarbarewar harkar tsaro a Arewacin kasar nan ba sabon abu ba ne, musamman ma ganin yadda ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kara tsananta a jihohin Arewa maso Yammacin kasar wadanda suka hada da Jihar Katsina da Jihar Zamfara da wani yanki na Jihar Kaduna.

Sai dai a ’yan kwanakin nan lamarin ya fara kutsawa Jihar Kano, inda a da can ba a cika samun lamarin ba, domin ko a makonnin da suka gabata an sace matar Dagacin garin Tsara da ke yankin Karamar Hukumar Rogo a cikin jihar inda ta shafe wasu kwanaki a hannun masu garkuwa da ita kafin daga baya ta shaki iskar ’yanci bayan iyalanta sun biya kudin fansa.

A makon da ya gabata ma a ranar 17 ga watan Nuwamba 2020 sai da Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Saleh Habib wanda ya yi garkuwa da wata yarinya mai suna Asiya Tasi’u ’yar kimanin shekara takwas da haihuwa a Karamar Hukumar Gabasawa wanda daga baya kuma ya hallaka ta bayan ya karbi kudin fansa Naira dubu 500 daga iyayenta.

4 thoughts on “‘Ayyukan ta’addanci na karuwa a Kano’

Leave a Reply