Uncategorized

BAKI SHI KE YANKA WUYA: Kotu Ta Daure Sadiya Haruna Wata Shida A Jarun

Daga: mohammed kaka Misau, Bauchi.
Kotu ta yanke wa Sadiya Haruna hukuncin zaman gidan yari har wata shaida (6) ba tare da zabi na biyan tara ba akan laifi da kotun ta sameta da shi na kiran mawakin Hausa Isah A Isah da dan iska, kawali, dan luwadi.

Sannan ta ce ya yi zina da ita kuma ta wallafa a shafinta na instagram.

Wannan matakin ya biyo bayan gurfanar da ita ne da aka yi a gaban kotun.

Idan za ku iya tunawa a baya-bayan nan an tursasa wa Sadiya Haruna komawa Islamiyya domin gyara dabi’unta.

Leave a Reply