Uncategorized

AN YANKA TA TASHI A KANO: Rikicin Cikin Gida Na APC A Kano Na Kara Ruruwa

Daga: mohammed kaka Misau, Bauchi.
Dangane da matakin da uwar jam’iyyar APC ta dauka dangana da bangarorin da suke musayar yawu da juna kan zaben shugabannin APC a matakin jihar Kano, bangaren G7 na su tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau sun yi watsi da matakin da uwa jam’iyyar ta dauka.

Lamarin da ke kara nuna cewa har yanzu da sauran rina a kaba wajen daidai lamuran siyasar jam’iyyar a jihar Kano duk kuwa da karatowar babban Taron jam’iyyar da ke tafe Nan da ‘yan kwanaki.

Leave a Reply