Uncategorized

Da Diminsa: Mataimakin Kakakin Majalisar Bauchi Ya Sha Kaye A Zaben Fid Da Gwani


Daga Khalid Idris Doya
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Honorable Danlami Ahmed Kawule ya sha kasa a zaben fitar da gwani na Dan Majalisar tarayya mai neman wakiltar mazabar karamar hukumar Bauchi a karkashin jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar.


Wakilinmu ya labarto mana cewa Alhaji Aminu Ali Garu shine ya kada Kawule da gagarumar nasara bayan fafata zaben da aka gudanar ta hanyar amfani da wakilai wato (delegates) a yau Lahadi a Bauchi.
Da ya ke bayyana farin cikinsa bisa wannan nasarar, Aminu Garu ya gode wa Allah bisa samun nasara da ya yi, ya kuma gode wa delegates bisa amincewa masa da zabinsa.


Ya kuma yi kira ga wadanda suka fafata neman kujerar tare da su wato sauran mutum biyun da suka fadi da su hada hannu wajen samun nasarar jam’iyyar a babban zaben 2023 da ke tafe. 


Duk kokarin da ‘yan jarida suka yi don jin ta bakin Kawule bisa wannan shan kayen da ya yi abun ya citura zuwa yanzu.


Wakilinmu ya nakalto cewa, shi dai mataimakin Kakakin Majalisar yanzu haka shine ke wakiltar mazabar Zungur, Galambi da Miri a Majalisar wakilai ta jihar, wanda tunin kuma jam’iyyar ta zabi wani a kan wannan kujerar da zai daga mata tutarta na neman wannan mazabar a zaben 2023. 

Leave a Reply