Uncategorized

Yanzu -yanzu Dan Majalisar Misau/Dambam Ya Janye Takarar Kujerarsa Kasa Da Awanni 24 Da Zaben Fidda Gwani

Daga Mohammed kaka Misau

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Misau/Dambam a Majalisa wakilai ta tarayya kuma dan takara a karkashin jam’iyyar PDP, Hon. Ibrahim Makama Misau ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar awanni kalilan da gudanar da zaben fitar da gwanaye na jam’iyyar.

Jaridar BAUSHETIMES ta ruwaito cewa an yi wannan bayanan ne ranar 22 ga watan Mayu 2022 daga maitamaka wa mai wakilin yankin na musamman Garba Modibbo jimkadan bayan jam’iyyar ta gudanar da wata zaman gaggawa a Misau yayin da yake amsa tambayoyi daga wakilinmu.

Garba Modibbo ya cigaba da bayyana cewa Ibrahim Makama ya janye ra’ayinsa ne a bisa gashin kansa saboda wasu dalilai da ba a ayyana ba, wanda bazai rasa nasaba da cigaban yankin sa ba.

Ta kara da cewa har yanzu su halartattun mambobin PDP ne, tare yin kira ga magoya bayan su dasu kasance ‘yan kasa masu bin doka sau da kafa.

Daga karshe ya ce, wakilin yankin nan bada dadewa ba zai bayyana manufarsa tare da dalilan sa na wannan janyewa.

Leave a Reply