Uncategorized

Da Dumi-Dumi: Dan Takarar Gwamnan Bauchi Na NNPP Ya Sha Mummunar Kasa A Karamar Hukumarsa

Daga Khalid Idris Doya

Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar NNPP, Sanata Halliru Dauda Jika ya kasa lashe zaben kujerar gwamna a karamar hukumarsa ta Ganjuwa inda PDP ta samu nasara.

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad luma dan takarar PDP shi ne ya samu nasarar lashe karamar hukumar da kuri’u 20,924.

A sakamakon da aka gabatar a a ranar Lahadi gaban Jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Bauchi, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya yi nuni da cewa shi dan takarar NNPP ya samu kuri’u 7,387 ne kacal a karamar hukumar sa ta haihuwa.

Kazalika, dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba ya samu kuri’u 17,606.

Wakilinmu ya labarto cewa zuwa yanzu kananan hukumomin da aka samu sakamakon su a hukumance na nuni da cewa dan takarar PDP ne ke kan gaba

Leave a Reply