Uncategorized

Da Dumi-dumi: Jonathan Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Hadimansa Biyu Sun Mutu A Hatsarin Mota

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan da yammacin yau Laraba ya gamu da tsautsayi na hatsarin mota a Abuja wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar hadimansa biyu, sai dai bayanai sun tabbatar da cewa Jonathan din na cikin koshin lafiya.

Daya daga cikin mukarrabansa ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya shaida cewar kawo yanzu dai shine Jonathan din na cikin koshin lafiya babu wani mummunar abu da ya sameshi.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton an ce tsohon Shugaban kasan yana gidansa.

Hatsarin motar ya rutsa da tsohon Shugaban kasar ne lokacin da ke kan hanyarsa ta komawa gida a Abuja daga filin jirgin kasa da kasa ta Nnamdi Azikiwe International Airport.

Leave a Reply