Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Shida: Falalar Karanta Alkur’ani

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya saukar da littatafai, don bayi su san Allah, su san shi da Siffofinsa, su san hakkokinsa a kansu, da shari’ar da za ta inganta musu rayuwa.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

‘Yan’uwa, karatun Alkar’ani yana cikin manyan aiyukan Ibada, Allah ya ce: {Lallai wadanda suke karanta littafin Allah, kuma suka tsayar da Sallah, suka ciyar daga abin da muka arzurta su a boye da bayyane suna fatan samun kasuwanci maras faduwa. Don Allah ya cika musu ladansu, ya kuma kara musu daga falalarsa, lallai shi mai gafara ne kuma mai godiya} [Fadir: 29 – 30].

Karatun Alkur’ani nau’i biyu ne:
Na farko: Karatu na hukunci, wanda ya kunshi gaskata labaran da ke cikinsa, da aiki da hukunce – hukuncensa na umurni da hani.

Na biyu: Karanta lafazinsa, nassoshi masu yawa sun zo suna bayanin falalarsa, imma karanta dukkan Alkur’anin ko kuma karanta wasu Surori ko wasu Ayoyi daga cikinsa. Ya abbata daga Usman (ra), Annabi (saw) ya ce: ((Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur’ani kuma ya koyar da shi)). Bukhari (5027).
Kuma ya tabbata ya ce: ((Kwararre a karanta Alkur’ani yana tare da Mala’iku SAFARA, KIRAMIN BARARA, amma wanda yake karanta Alkur’anin amma yana i’inna a cikinsa, karatun yana wahalar da shi yana da lada biyu)). Bukhari (4937), Muslim (798).
Ma’ana; lada daya na karatun, dayan kuma na wahalar da ya sha a kan karatun.
Haka ya tabbata daga Abu Musa al-Ash’ariy, Annabi (saw) ya ce: ((Misalin Muminin da yake karanta Alkur’ani kamar tanjirin ne, kamshinsa dadi, dandanonsa ma dadi. Misalin Muminin da ba ya karanta Alkur’ani kamar dabino ne, ba shi da kamshi dandanonsa kuma zaki)). Bukhari (5020), Muslim (797).
Ya tabbata Annabi (saw) ya ce: ((Ku karanta Alkur’ani, don zai zo ya ceci ma’abotansa a Ranar Qiyama)). Muslim (804).
Haka ya tabbata daga Uqba bn Amir, Annabi (saw) ya ce: ((Da dayanku zai tafi Masallaci ya koyi karatu, ko ya karanta Ayoyi biyu na littafin Allah hakan ya fi a ba shi rakuma biyu, ya karanci Aya uku ya fi masa rakuma uku, ya karanci Aya hudu ya fi masa rakuma hudu, ya fi masa rakuma masu yawa)). Muslim (803).
Haka kuma ya tabbata daga Abu Huraira (ra) Annabi (saw) ya ce: ((Mutane ba za su hadu a daki daga cikin dakunan Allah ba, suna karanta littafin Allah, suna yin darasinsa a tsakaninsu face nitsuwa ta sauka a kansu, rahma ta lullube su, Mala’iku sun kewaye su, kuma Allah ya ambace su a cikin wadanda suke wajensa)). Muslim (2699).
Kuma ya ce: ((Ku lazimci karanta Alkur’ani, na rantse da wanda raina ke hanunsa ya fi rakuma kubucewa daga igiyarta)). Bukhari (5033), Muslim (791).

Ya tabbata Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda ya karanta harafi daya na littafin Allah yana da kyakkyawan aiki daya, kuma za a ninka shi gida goma. Ba ina nufi Alif, Lam, Meem harafi ne da ya ba, a’a, “Alif” harafi ne, “Lam” harafi ne, “Meem” harafi ne )). Tirmiziy (2910).

‘Yan’uwa wadannan su ne falalolin karanta Alkur’ani, kuma ga bayanin ladansa a wajen Allah, lada mai yawa a kan aiki mai sauki, wanda ya yi sakaci ya yi hasaran lada mai yawa.

Haka wasu Hadisan sun zo da bayanin falalolin wasu Surori, kamar Suratul Fatiha, Suratul Baqarah da Ali Imran, Suratul Ikhlas, da Kula’uzai. Haka akwai Hadisai a kan falalolin wasu Ayoyi, kamar Ayatul Kursiyyi da sauransu.

Don haka ya ku ‘Yan’uwa, ku dage da yawaita karatun Alkur’ani a cikin wannan wata mai girma, watan da a cikinsa aka saukar da Alkur’ani. Kuma Mala’ika Jibril (as) ya kasance duk shekara a Ramadhan yakan zo wajen Annabi (saw), Annabi yana bitan Alkur’ani a wajensa. Amma a shekarar rasuwarsa sau biyu ya zo masa, kamar yadda ya tabbata daga Ibnu Abbas (ra) ya ce:
((Annabi (saw) ya kasance ya fi kowa kyauta, kuma kyautansa ya fi yawa a Ramadhan, saboda Jibril ya kasance yana haduwa da shi a kowane dare a watan Ramadhan har ya kare, Manzon Allah (saw) yana karanta masa Alkur’ani, idan Jibril ya hadu da shi ya kasance mafi kyauta fiye da iska mai kadawa)). Bukhari (4997), Muslim (2308).

Wannan ya sa Magabata sukan yawaita karanta Alkur’ani a cikin watan Ramadhan, al-Zuhriy idan Ramadhan ya shiga yake cewa: watan karatun Alkur’ani da ciyar da abinci. Imam Malik ya kasance idan Ramadhan ya shiga yakan dena karantar da Hadisi da majalisan ilimi, ya fisknaci karatun Alkur’ani.
An ruwaito Qatada ya kasance yana sauke Alkur’ani a dare bakwai, amma a Ramadhan a dare uku yake saukewa, a goman karshe kuma yana saukewa a kowane dare. Ibrahim al-Nakha’iy kuma yana sauke Alkur’ani a Ramadhan a kowane dare uku, a goman karshe kuma yana saukewa a kowane dare biyu. Haka al-Aswad yana sauke Alkur’ani a kowane dare biyu a watan gaba daya.

Don haka ‘yan’uwa ku yi koyi da wadannan Magabata na kwarai, ku ribaci wannan wata ta hanyar yawaita karanta Alkur’ani dare da rana, hakan zai kara muku kusaci ga Ubangijinku.

Allah ya taimake mu a kan aiyukan da’a, ya sa mu dace da falalolin wadannan aiyukan Ibada, ya ba mu dukkan albarkatu da suke cikin wannan wata.

‘Yan’uwa kar mu manta da kasarmu Nigeria, mu yawaita rokon Allah a kan ya ba mu zaman lafiya, ya kawar mana da fitinar ta’addanci da garkuwa da mutane, ya ba mu arziki da shugabanni na gari masu tsoron Allah, masu tausayin talakawa.

Leave a Reply