Uncategorized

Na sauya sheƙa daga APC zuwa PDP saboda na ceto Al’umma ta- DAN-Makaman.


Daga: Mohammed kaka Misau, Bauchi
Mamba dake wakiltar mazabar Misau da Damban a majalisar wakilai ta tarayya Ibrahim Makama Misau ya bayyana cewa yabar tsohuwar Jam’iyyar sa ta APC ne sakamakon irin tarin matsalolin dake cikin Jam’iyyar musamman kafin babban taron da jam’iyyar APC ta gudanar da Kuma bayan sa.

Dan majalisar ya bayyana irin rashin bin tsari da kwamachalar daya faru a lokacin babban taron jam’iyyar daya gudana, a cewar sa na daya daga cikin dalilan da ya sanya shi fita daga jam’iyyar.

Garba Modibbo na daga cikin hadiman Dan majalisa Mai wakiltar mazabar Misau da Damban a majalisar wakilai ta tarayya ya kara da cewa jin kadan bayan kammala taron jam’iyyar APC na kasa, Makaman Misau ya Kira taron Tattaunawa tare da Jagororin sa na gundumomi Ashirin (20) dake mazabar sa, a inda kashi Chasa’in cikin dari suka nuna goyon bayan su na ficewa a jam’iyyar APC domin nuna rashin amincewar su da abinda jam’iyyar APC ta musu a mazabar Misau da Dambam.

Yace bayan nan sun yi zaman Tattaunawa tare da masu ruwa da tsakani a Matakin Misau da Dambam dangane da yadda za’a shawo kan matsalolin dake addabar jam’iyyar ciki harda takaddamar dake gaban kotu, Amma abin yaci tura, Saboda haka ya yanke wannan hukunci domin tsoron kar abinda ya faru da Jam’iyyar su a jihar Zamfara a zaben da ya gabata na 2019.

Ya kara da cewa Jagororin sane suka neme shi daya koma jam’iyyar PDP lura da irin aikin gina kasa da Gwamnan jihar Bauchi Gwamna Bala Abdulkadir yake aiwatarwa.

Dan majalisar ta bakin Kakakin sa ya kara da cewa lura da aniyar gwamnan na ganin ya tallafi Al’ummar jihar Bauchi yasa yaga bashi da wani zabi illa Shima ya shigo jam’iyyar domin tunda ra’ayin Al’ummar sane.

Yace ba ya dawo PDP domin samun tikiti na kai tsaye bane kamar yadda wasu ke yada jita jita a kan hakan, ya kara da cewa babu dole ga duk Wanda daga cikin mutanen sa yaga ba zai iya binsa cikin jam’iyyar PDP ba.

Yace a halin yanzu zaben fidda gwani ya kusa na da ranar 2 ga watan 6 na wannan shekara amma har yanzu jam’iyyar APC ta kasa shiryawa hakan.

“A saboda haka tunda basu shirya ba, bamu da wani zabi illa kawai mu nemi wata domar domin cigaban Al’ummar mu.”

A halin yanzu dai Dan majalisar Hon. Ibrahim Makama Misau ya sayi fom din tsayawa takarar kujerar da a yanzu yake kai na Misau da Dambam a karkashin jam’iyyar PDP domin sake neman kujerar tasa a zabe me zuwa na 2023.

Leave a Reply