DARUSAN RAMADHAN
Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia
Darasi na Bakwai: Hukunce-hukuncen mutane a cikin Azumi (1)
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
‘Yan’uwa, ya gabata cewa; farlanta Azumi ya kasance ne a matakai guda biyu, sai kuma ya tabbata a kan farlanci a kan kowa ba tare da bayar da zabi ba. Don haka mutane suka kasance kashi goma a cikin Azumin:
Kashi na farko:
Musulmi baligi mai hankali mai iko a kan yin Azumin, to wannan Azumin Ramadhan ya wajaba a kansa, dole ya yi Azumin a kan lokacinsa, wato watan Ramadhan. Saboda fadin Allah: {Duk wanda ya halarci watan a cikinku to wajibi ne ya azumce shi}. [al-Baqarah (185)].
Da fadin Annabi (saw): ((Idan kun ga jinjirin watan to ku yi Azumi)). Bukhari (1907) Muslim (1080).
Kuma Malamai sun yi Ijma’i a kan wajabcin Azumin Ramadhan a kansa.
Amma kafiri Azumi ba ya wajaba a kansa, saboda ba shi da sharadin ingancin Ibada, wato Muslunci. Don haka idan ya muslunta a tsakiyan watan Ramadhan to ramukon kwanakin da suka gabata bai hau kansa ba. Amma a ranar da ya muslunta dole ya kame bakinsa har zuwa faduwan rana, ba zai cigaba da cin abinci ba, don ya zama cikin wadanda Azumi ya wajaba a kansa, kuma ramukon wannan Azumi na wannan rana da ya muslunta a cikinta bai wajaba a kansa ba.
Kashi na biyu:
Yaro karami, Azumi bai wajaba a kansa ba har sai ya balaga, saboda Annabi (saw) ya ce: ((An dage Alkalami a kan mutane uku; mai bacci har sai ya farka, yaro har sai ya yi mafarki, mahaukaci har sai ya yi hankali)). Abu Dawud (4403), Nasa’iy (3432), Ibnu Majah (2042).
Amma duk da haka an so wadanda suke kula da shi su sa shi yin Azumin idan zai iya yi, don ya saba tun kafin ya balaga, koyi da Magabata, don Sahabbai sun kasance suna umurtan ‘ya’yansu suna yin Azumi, alhali ba su balaga ba, kuma suna tafiya da su Masallaci da kayan wasa, idan sun yi kuka sai a ba su abin wasa ya dauke musu hankali.
Yaro yana balaga ne da dayan abubuwa guda hudu:
1) Fitowan maniyyi ta hanyar mafarki ko waninsa.
2) Tsiran gashi a gabansa.
3) Cika shekara goma sha biyar.
4) Zuwan jinin haila ga mace.
Don haka idan yaro ya balaga da rana kuma yana Azumi to sai ya cika Azuminsa, idan kuma ba ya Azumi to wajibi ne ya kame baki, kuma ramukon Azumin wannan rana da ya balaga a cikinsa bai wajaba a kansa ba.
Kasha na uku:
Mahaukaci, wato maras hankali, Azumi bai wajaba a kansa ba, saboda Hadisin da ya gabata. Kuma ko ya yi Azumi bai inganta daga gare shi ba, saboda ba shi da hankalin da har zai iya hankaltar Ibada da niyyarta. Saboda Annabi (saw) ya ce: ((Kawai aiyuka sai da niyya)). Bukhari (1), Muslim (1907).
Idan kuma haukan nasa lokaci – lokaci ne, to Azumi yana wajaba a kansa a lokacin da yake cikin hankalinsa. Idan kuma yana cikin Azumin sai haukan ya kama shi da rana, to Azuminsa bai baci ba, duk lokacin da ya dawo cikin hayyacinsa zai cigaba da Azuminsa. Haka idan ya wayi gari a cikin hauka, sai tsakiyan rana hankalinsa ya dawo, sai ya kame baki har faduwar rana, kuma babu ramuko a kansa, kamar yadda ya gabata a hukuncin kafirin da ya muslunta ko yaron da ya balaga a tsakiyar rana.
Saboda haka shi ma Mahaukaci babu ramuko a kansa na ranakun da ya kasance cikin hauka a cikinsu.
Kashi na hudu:
Tsohon da ya fara sunbatu, wanda ya zama ba ya iya banbance abubuwa shi ma Azumin bai wajaba a kansa ba, haka ciyarwa bai wajaba a kansa ba, saboda ya zama kamar yaro, hukuncin Shari’a ya fadi a kansa.
Amma idan sunbatun nasa lokaci-lokaci ne, to Azumi ya wajaba a kansa a lokacin da yake cikin hayyacinsa, haka Sallah ma kamar Azumi take a kansa.
Kashi na biyar:
Kasasshe wanda gaba daya ba zai iya yin Azumi ba, imma saboda girma ko rashin lafiyan da ba a zaton warkewarsa, kamar mai ciwon kansa da makamancinsa, to wannan ma Azumi bai wajaba a kansa ba, saboda ba zai iya yi ba. Allah ya ce: {Ku ji tsoron Allah gwargwadon iyawarku} [al-Tagabun: 16], ya ce: {Allah ba ya dora ma rai sai abin da za ta iya yi} [al-Baqarah: 286].
Sai dai ciyarwa ya wajaba a kansa a madadin yin Azumin, kowace rana zai ciyar da miskini, saboda a farko lamari na shar’anta Azumi, Allah ya sanya ciyarwa yana daidai da Azumi, ya kasance mutum yana da zabi tsakanin Azumi ko ciyarwa, don haka idan mutum ya kasa yin Azumi sai ya koma kan ciyarwa.
Mutum yana da zabi a ciyarwan, imma ya raba wa Miskinai, kowa ya ba shi mudu daya, daya bisa hudun sa’i, ko ya dafa abincin ya kira Miskinan ya ciyar da su, gwargwadon yawan ranakun Azumin. Ya zo cikin Bukhari: ((Tsoho idan ba zai iya yin Azumi ba zai ciyar, Anas (ra) bayan ya girma, ya ciyar a Azumin shekara daya ko biyu, kowace rana yana ciyar da miskini gurasa da nama, sai ya sha Azumi a ranar)). Sahihul Bukhari (6/ 25).
Ibnu Abbas ya ce: ((Tsohon da ya girma ko tsohuwa, wadanda ba za su iya yin Azumi ba za su ciyar da miskini a madadin kowace rana)). Bukhari (4505).
‘Yan’uwa, ku duba hikimar Allah cikin Shari’arsa, ta yadda ya shar’anta hukuncin da ya dace da kowane nau’i na mutane, tare da rahma, ta yadda ya saukaka ma kowane kashi na mutane, kowa an shar’anta masa gwargwadon ikonsa da iyawarsa, ya wajbata masa abin da ya dace da yanayinsa, don kowa ya samu ikon bauta ma Allah da sakakkiyar zuciya, da yarda da Allah da Addininsa da Manzonsa.
Lallai wannan Shari’a ta Muslunci tana tabbatar da samuwar Allah da tabbatar Siffofinsa, saboda duk wanda ya yi nazari cikin wannar Shari’a ta Muslunci to zai ga Shari’a ce wacce ta siffantu da hikima da rahma, abin da yake tabbatar da cewa; lallai Shari’a ce daga Allah Ubangiji mai ilimi da hikima da rahma. Don haka Shari’ar Muslunci tana tabbaar da samuwar Allah da tabbatar Sifofinsa.
Don haka ya wajaba mu gode ma Allah a kan rahmarsa da falalarsa a kanmu da wannar Shari’a mai cike da hikima da rahma, mai cike da dalilai masu nuna girman Allah da Siffofinsa na kamala. Mu gode ma Allah da ya shar’anta mana Shari’a wacce ta dace da yanayin kowa, don rahmarsa gare mu, yana so kowa ya bauta masa, don ya samu yardarsa da falalarsa da sakamakonsa a Ranar Lahira.
Ya Allah ka shiryar da mu ga yi maka da’a, da barin saba maka, ka ba mu ikon canzawa don halin da muke ciki na kuncin rayuwa da tsoro da rashin tsaro a kasarmu Nigeria ya canza zuwa halin arziki da wadata da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Allah ya jikan iyayenmu, da Malamanmu, ya karba mana ibadunmu, ya sa mu cika da Imani.