Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Takwas: Hukunce-hukuncen mutane a cikin Azumi (2)

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

‘Yan’uwa, bayanin kashe-kashe biyar na hukunce-hukuncen mutane a Azumi ya gabata, ga cigaba da kamar haka:

Kashi na shida:
Matafiyi sawa’un tafiyar mai tsawo ce ko gajeruwa, tafiya ce mai bijirowa ko tafiya ce ta kullum, kamar ta direbobin motocin haya, yana da zabin yin Azumi ko shan Azumin, matukar ba ya yi tafiyar ce da niyyar yin dabara ma Shari’a ba, idan ya yi da niyyan haka ya aikata haramun. Dalili a kan haka shi ne fadin Allah: {Duk wanda ya kasance maras lafiya ko yana halin tafiya to ya kirga Azumin a wasu ranakun daban, Allah yana so muku sauki ba ya so muku wahala}. [al-Baqarah (185)].
Ya tabbata daga Anas bn Malik (ra) ya ce: ((Mun kasance muna tafiya tare da Annabi (saw), amma mai Azumi ba ya aibanta wa maras Azumi, maras Azumi ba ya aibanta wa mai Azumi ba)) Bukhari (1947), Muslim (1118).
Abu Sa’eed al-Kudriy yana ba da labarin Sahabbai sukan fita yaki tare da Annabi (saw), a cikinsu akwai mai Azumi, akwai maras Azumi, sai ya ce: ((suna ganin wanda ya samu karfin yin Azumin sai ya yi to abu ne mai kyau, wanda kuma ya samu raunin yin Azumin sai ya sha Azumin shi ma abu ne mai kyau)). Muslim (1116).

Abin da ya fi dacewa ga dereban motar haya wanda Azumi zai yi masa wahala shi ne; idan Azumin a lokacin zafi ne to sai ya sha Azumin, sai ya rama a lokacin sanyi.
Abin da ya dace ga Matafiyi shi ne ya yi abin da ya fi masa sauki, imma ya yi Azumin idan ba zai samu rauni ba, ko kuma ya sha Azumin idan zai yi rauni. Idan kuma duka daya ne a gare shi to abin da ya fi ya yi Azumin, saboda idan ya yi ya sauke nauyin da ke wuyansa, kuma ya yi Azumi tare da mutane, zai fi samun nishadi, saboda hakan shi ne aikin Annabi (saw), kamar yadda ya tabbata daga Abu al-Darda’i ya ce: ((Mun fita tare da Manzon Allah (saw) a Ramadhan, a cikin tsananin zafi, har ya kai ga dayanmu yana dora hanunsa a kansa saboda tsananin zafi. Alhali babu mai Azumi a cikinmu sai Manzon Allah (saw) da Abdullahi bn Rawaha (ra))). Muslim (1122).
Kuma Annabi (saw) ya karya Azuminsa don saukaka wa Sahabbansa, a lokacin da labari ya same shi cewa; Azumin ya wahalar da mutane, kamar yadda ya tabbata daga Jabir (ra) ya ce: ((Manzon Allah (saw) ya fita zuwa Makka a shekarar fathu Makka, sai ya dauki Azumi, har sai da ya isa wani waje da ake kira KURA’U al-GAMEEM, kuma mutane suna Azumi, sai ya sa a kawo masa kokon ruwa, sai ya daga shi sama, har mutane suka gani, sai ya sha)) Muslim (1114).

Don haka Matafiyi idan Azumi zai wahalar da shi to sai ya sha Azumin, kar ya ce zai yi Azumin, saboda Annabi (saw) ya karya Azuminsa saboda Azumin ya yi wahala wa mutane, amma sai aka ba shi labarin wasu ba sun yi Azumin, sai ya ce: ((Wadannan su ne masu sabo, wadannan su ne masu sabo)). Muslim (1114).
A wani Hadisin kuma ya ce: ((Azumi a cikin tafiya ba ya cikin da’a ma Allah)). Bukhari (1946), Muslim (1115).

Idan mutum ya taso daga wani gari zai dawo garinsu, kuma ya sha Azumi saboda tafiya, sai ya iso garinsu da rana, zai kame baki a wajen wasu Malamai, amma jamhurin Malamai sun tafi a kan ya halasta gare shi ya ci, ya sha, sai dai bai kamata ya kasance a gaban mutane ba.

Kashi na bakawai:
Maras lafiyan da ake fatan zai warke, wannan yana da halaye uku:
Na farko: Idan Azumin ba zai cutar da shi ba, kuma ba zai wahalar da shi ba to ya wajaba ya yi Azumi.
Na biyu: Idan Azumin zai wahalar da shi, amma ba zai cutar da shi ba, wannan ya halasta gare shi ya sha Azumin, sai ya rama idan ya samu sauki, saboda Ayar da ta gabata. Makruhi ne ya yi Azumi matukar zai wahala, saboda ya samu rangwame daga Allah, Annabi (saw) ya ce: ((Lallai Allah yana so a yi aiki da ramgwamensa kamar yadda yake kin a aikata sabonsa)). Ahmad (5866), Ibnu Khuzaimah (2017), Ibnu Hibban (354).
Na uku: Idan Azumin zai cutar da shi to ya wajaba ya sha Azumin, bai halasta ya yi Azumin ba. Saboda Allah ya hana jefa kai cikin halaka, kuma Shari’a ba ta zo da wahalarwa ba.

To shi wannan maras lafiya zai yi lissafin ranakun da ya sha Azumin, idan ya warke sai ya rama su.

Allah ya ba mu lafiya, ya karba mana ibadunmu a cikin wannan wata mai albarka.

Leave a Reply