Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Tara: Hukunce-hukuncen mutane a cikin Azumi (3)

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Bayani a kan kashi na bakwai ya gabata, ga cigaba kamar haka:

Kashi na takwas:
Mace mai haila: haramun ne mace mai jinin al’ada ta yi Azumi, kuma ko ta yi bai inganta ba, saboda Annabi (saw) ya ce: ((Ban ga masu tauyayyen hankali da Addini mai jan hankalin tsayayyen namiji kamar daya daga cikinku ba”. Sai suka ce: Menene tawayan hankali da Addinin namu ya Manzon Allah? Sai ya ce: “Shin shaidar mace ba rabin na namiji ba ne?” suka ce: Eh haka ne. Ya ce: “To wannan shi ne tawayan hankalinsu. Kuma shin ba tana barin Sallah da Azumi ba idan tana jinin haila?”, suka ce: Eh tana bari. Ya ce: “To wannan shi ne tawayan Addininsu”)). Bukhari (304) Muslim (79).

Idan jinin haila ya zo wa mace alhali tana Azumi, ko da kusa da faduwar rana ce da minti daya, to Azuminta na wannan rana ya baci, ramuko ya kama ta, sai dai idan Azumin nafila ne, ramukonsa ba wajibi ba ne.
Haka idan ta yi tsarki daga haila da rana a Ramadhan ba ta da Azumin wannan rana. Amma shin za ta kame baki? Amsa a kan haka ya gabata a bayanin hukuncin matafiyin da ya dawo gida da rana. Jamhurin Malamai sun tafi a kan cewa; ba wajibi ba ne.
Idan kuma ta yi tsarki cikin dare, ko da kafin al-fijr da minti daya ne to Azumi ya wajaba a kanta. Za ta dauki Azumi ko da ba ta samu daman yin wanka ba, sai bayan fitowan al-fijr. Hukuncinta kamar hukuncin mai janaba ne, ya tabbata daga A’isha (ra) ta ce: ((Annabi (saw) ya kasance yana wayan gari yana mai janaba, saboda saduwa da iyali, kuma ya dauki Azumi)). Bukhari (1931) Muslim (1109).

Mai jinin haila wajibi ne ta rama Azumin ranakun da ba ta yi Azumi ba saboda zuwan jinin, an tambayi A’isha (ra): Me ya sa mai haila take rama Azumi, amma ba ta rama Sallah? Sai ta ce: ((Hakan yana faruwa da mu sai a umurce mu da mu rama Azumi, amma ba a umurtanmu da rama Sallah)). Muslim (335).

Mai jinin biki hukuncinta kamar mai jinin haila ne, cikin dukkan hukunce-hukunce da suka gabata.

Kashi na tara:
Mace mai shayarwa: idan mace ta kasance mai shayarwa ko mai ciki, sai ta ji tsoron za ta cutu idan ta yi Azumin, ko kuma dan nata zai cutu, to ya halasta ta sha Azumin, saboda Hadisin Anas bn Malik (ra), Annabi (saw) ya ce: ((Allah ya dauke wa mai Matafiyi rabin Sallah, ya dauke Azumi wa matafiyi da mai ciki da mai shayarwa)). Abu Dawud (2408), Tirmiziy (715), Nasa’iy (2275), Ibnu Majah (1667).
Don haka ya halasta ta sha Azumi, kuma wajibi ne ta rama ranakun da ta sha.

Kashi na goma:
Mabukaci zuwa ga shan Azumi: wanda ya bukaci shan Azumi saboda wata larura, kamar tsamar da wanda ya nitse a ruwa, ko kubutar da wanda gobara ta ritsa da shi, ko wanda gini ya rushe a kansa, ko wanda ya makale a sama, ko ya fada rijiya, ko taimakon masu hatsarin mota da makamantan haka, idan ya zama ba zai iya kubutar da dayan wadannan ba har sai ya ci abinci ko shan ruwa, don ya samu karfin jiki to ya halasta ya sha Azumin, ya ma wajaba, don kubutar da wanda ya fada cikin halaka wajibi ne. Kuma ya wajaba ya rama Azumin.

Haka sojojin Muslunci da suke wajen Jihadi saboda Allah, wajen yakar abokan gaban Musulmai, ya halasta su sha Azumi don su samu karfin yin Jihadi, kuma za su rama. Saboda Hadisin da ya abbata daga Abu Sa’eed (ra) ya ce: ((Mun yi tafiya tare da Manzon Allah (saw) zuwa Makka, alhali muna Azumi, sai muka sauka a wani wajen, sai Manzon Allah (saw) ya ce: “Hakika kuna kusa da abokan gabanku, shan Azumi zai ba ku karfin jiki”, wannan rangwame ne, a cikinmu akwai wadanda suka yi Azumi, akwai kuma wadanda suka sha Azumin. Sai muka sake sauka a wani wajen, sai Manzon Allah (saw) ya ce: “Lallai za ku dirar ma abokan gabanku da safe, shan Azumi zai ba ku karfin jiki, don haka ku sha Azumi”, wannan sai ya zama umurni na dole, sai duka muka sha Azumin)). Muslim (1120).
Wannan Hadisi yana nuni ga cewa; samun karfin yakar abokan gaba shi ma sababi ne mai cin gashin kansa da zai sa a sha Azumi, ba dole sai da sababin tafiya ba.

Dukkan wanda ya halasta ya sha Azumi cikin wadanda ambatonsu ya gabata to wajibi ne ya rama Azumin kwanakin da ya sha Azumin Ramadhan. Wanda ya sha watan gaba dayansa, zai rama watan. Idan watan kwana talatin ya yi Azumi talatin zai rama, haka idan ishirin da tara ya yi.

Ana so mutum ya gaggauta rama Azumin Ramadhan da yake kansa, kar ya jinkirta shi har watan Sha’aban idan ba tare da uzuri ba. Ya tabbata daga A’isha (ra) ta ce: ((Azumin Ramadhan yakan kasance a kaina, amma ba na iya ramawa har sai a Sha’aban, saboda shagaltuwa da hidima wa Manzon Allah (saw))). Bukhari (1950), Muslim (1146).

Amma idan uzurin bai gushe ba, har mutuwa ta riske shi, to babu komai a kansa. Amma idan sakaci ya yi, danginsa sai su rama masa, saboda ya tabbata Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda ya mutu akwai Azumi a kansa majibintansa su rama masa)). Bukhari (1952) Muslim (1147).

Wadannan su ne kashe-kashen mutane a cikin Azumi, Shari’a ta zo da hukuncin kowa gwargwadon yanayi da halin da yake ciki, saboda rahma da hikima da suke cikin Shari’ar Allah Mai hikima da rahma. Don haka sai mu gode wa Allah a kan haka, mu roke shi tabbatuwa a kan bin Shari’arsa da yi masa da’a don neman yardarsa.

Allah ya karba mana, ya gafarta mana zunubanmu, ya jikan iyayenmu, ya kyautata karshenmu, ya ba mu zaman lafiya, ya yi mana maganin matsalolin tattalin arziki da na tsaro da muke fama da su a kasarmu.

3 thoughts on “DARUSAN RAMADHAN

Leave a Reply