Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na farko: Falalan watan Ramadhan

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya yi halitta, kuma ya arzurta ta, Ubangijin kowa da komai, kuma masanin komai. Ya yi ni’imomi masu yawa ga halitta, daga cikin ni’imominsa gare su ya halicci mutane don su bauta masa, kuma ya aiko musu Manzannin don su koyar da yadda za su yi bautar, ya saukar da Littatafai wadanda suka kunshi bayanin hukunce-hukuncen Shari’a da bayanin bauta. Daga cikin Ni’imominsa ga mutane ya aiko musu Annabi Muhamad (saw) a matsayin rahma ga talikai, ya saukar musu da Alkur’ani a matsayin bayani da shariya ga hanya madaidaiciya.

Allah ya yi tsira da aminci ga wannan Manzo, wanda ya yi bayanin Addini ga al’ummarsa, ya bayyana mata hanyar shiriya, hanyar tsira, ya bayyana mata komai na Addini da abin da take bukata na rayuwa, ya bar al’umma a kan hanya bayyananna, har dare ya zama a bayyane kamar rana.

Ya kai dan’uwa Musulmi, hakika Allah ya yi maka ni’ima da ya kawo ka wannan wata na Ramadhan a wannan shekara, wata mai albarka, lokacin aiyukan Ibada masu falala. Allah yana girmama ladan Ibada a cikinsa, yana bude kofofin alheri, ya rufe kofofin sharri. Watan alherai da albarkatu. Watan kyauta da baiwa, watan da yake cike da rahma da gafara da ‘yanta bayi daga wuta. Farkonsa rahma ne, tsakiyansa gafara, karshensa ‘yanta bayi daga wuta.

Hadisai sun zo suna bayanin falalar wannan wata na Ramadhan, daga cikinsu akwai Hadisin Abu Huraira (ra) ya ce: Ma’aikin Allah (saw) ya ce: ((Idan watan Ramadhan ya shigo akan bubbude kofofin Aljanna, a rurrufe kofofin Jahannama, kuma a daure shaidanu da kaca)).
Sahihul Bukhari (1899), Sahihu Muslim (1079).

Ana bude kofofin Aljanna a wannan wata ne saboda yawan kyawawan aiyuka a cikinsa, da kwadaitar da bayi masu aiki. Ana rufe kofofin wuta saboda karancin aiyukan sabo daga bayin Allah masu Imani. Kuma ana daure shaidanu a hana su samun abin da suke samu asauran watannin.

‘Yan’uwa, ya kamata mu san cewa; samun watan Ramadhan ni’ima ce mai girma ga wanda ya tsaya ya bai ma watan hakkinsa na yawaita Ibadu da aiyukan alheri a cikinsa, da nisantar aiyukan sabo, da rashin gafala daga zikiri da ambaton Allah, da yawaita karatun Alkur’ani, saboda watan Ramadhan watan Alkur’ani ne. Allah ya ce: {Watan Ramadhan wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa shiriya ne ga mutane da bayanin shiriya da rarrabewa}. Baqara (Aya: 185).

Don haka dan’uwa kar ka yi sakaci ka yi asaran falaloli da alherai da albarka da suke cikin wannan wata mai falala. Ka zage damtse ka yawaita Ibada a cikinsa, tare da tsarkake niyya, ka nemi falalolin Ubangijinka wadanda ya cika wannan wata da su.

4 thoughts on “DARUSAN RAMADHAN

Leave a Reply