Uncategorized

2023: Zan Sake Tsayawa Takarar Dan Majalisar Jiha, Inji Hon. Bobbo

Daga Abubakar Muhammadu

Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Hon. Bakoji Aliyu Bobbo ya bayyana cewar zai sake neman kujerar dan Majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar kasar Ciroma a karamar hukumar Misau a Majalisar jihar domin daurawa daga inda ya faro a yayin babban zaben 2023 da ke tafe.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ke ganawa da shugabanni PDP da ke kasar Ciroma a dakin taro na Chartwell jiya, ya ce hakan ya biyo bayan shawarori da ya yi da goyon bayan sa da kuma makusanta inda suka karfafeshi kan hakan Wanda hakan ta sanya ya yanki fom din takarar.

Hon. Bakoji Aliyu har-ila-yau ya yi godiya wa al’ummar kasar Ciroma tare da kara zayyana musu nasarorin da ya cimma yayin shugabancin nasa sai ya shaida musu cewa hakan ba zai hana a ce ya tafka kuskure ba a matsayin na dan adam wanda yake tara bai cika goma ba.

Hon. Bobbo sai ya ce kafin bayyana matsayan sa sai da ya gana da shugaban PDP kan idan da akwai dan takara da ya fi shi dacewa da kujerar shi ma zai mara mai baya domin cigaba yankin.

Daga karshe shugababbin jam’iyyar PDP sun nuna masa cewa basu da wanda ya fi shi cancanta kawo yanzu. Don haka ya dace da wannan kujera na wakilcin Ciroma a majalisar jiha.

Shugaban jam’iyyar ta PDP na karamar hukumar Misau, Alhaji Abdu Haruna ya bayyana himmatuwar shugaban marasa rinjayen na ganin ya kawo ingantacciyar wakilci da samar da ayyukan yi ga al’umman yankin Ciroma da Misau baki dayansu.

Shugaban sai ya shaida masa cewa jam’iyyar PDP za ta masa karanci wajan tabbatar da shi akan karagar kujerar a zabe mai tafe saboda kokari da himma da yake da shi.

A nasu jawaban daban-daban Hon. Bashir Tahir tsohon dan takaran majalisar dokoki na jihar Bauchi na yanki Ciroma a jam’iyyar NNPP a zaben 2019 da Alh. Babangida Turak, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Misau kana tsohon mamba ta jiha sun bayyana Hon. Bobbo a matsayin jajitaccen mutum tun a baya da ya rike kujeru mabanbanta tare da yin addu’ar Allah ya ba shi sa a a zabe mai zuwa.

Suma a nasu gudumawar Hon. Umar Baba Misau tsohon dan majalisar dokokin jihar Bauchi na yankin Ciroma daga shekarar 1999-2003, da Hon. Usman Abdu Misau, tsohon sakataren karamar hukumar Misau na riko, da Malama Asabe Jauro sun yi jawabin goyan baya ga shi Hon. Bobbo tare da kiran al’umman yankin Ciroma da su zabe shi a shekarar 2023 dake zuwa.

Leave a Reply