Uncategorized

Duk Da Nemansa Ruwan A Jallo Da ‘Yansanda Ke Yi, Dan Majalisa, Shehu Ya Halarci Rufe Yakin Neman Zabe

Daga Khalid Idris Doya

Dan majalisar wakilai ta tarayya da ke wakiltar mazabar cikin garin Bauchi, Alhaji Shehu Abdullahi ya bayyana a bainar jama’a a yau Alhamis duk da cewa rundunar ‘yansanda ta kasa ta ayyana nemansa ruwa a jallo.

Idan za ku iya tunawa dai kwanaki kalilan da suka wuce ne ‘yansanda suka shelanta neman Yakubu Shehu Abdullahi ruwa a jallo bisa zarginsa da hannu a rikicin siyasa da ya barke a kauyen Duguri da ke Alkaleri kwanaki.

Wakilinmu ya labarto cewa an ga Shehu a cikin tawagar yakin neman zaben dan takarar Gwamnan na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar sa’ilin da suke rufe kafen a yau Alhamis hankalinsa kwance yana shelar a zabi APC tare da rakiyar daruruwan matasa.

Tawagar ta zaga manya da kananan titinin kwaryar jihar tare Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na APC, Sadiq Abubakar, da tsohon Kakakin Majalisar Dokokin tarayya, Yakubu Dogara da wasu jiga-jigai na APC.

Kodayeke wata majiya ta tsegunta ma wakilinmu cewa ana harsashen Yakubu Shehu din ya samo wata umarnin kotu da ta dakatar da ‘yansandan da ka cafke shi.

Leave a Reply