Gidauniyar Ali Usman Ta Rabar Da Littafan Rubutu Miliyan 1 Ga Daliban A Bauchi Ta Kudu
Daga Khalid Idris Doya
Gidauniyar Hon. Ibrahim Ali Usman ta rabar da kyautar littafan rubutu guda miliyan 1,050,000 a yankin Bauchi ta Kudu a ƙoƙarinta na bunƙasa harƙoƙin ilimi da taimaka wa harƙokin karatun yara a yankin.
Gidauniyar ta rabar da littafan rubutu guda 150,000 a kowace ƙaramar hukuma bakwai da suke yankin Sanatan Bauchi ta Kudu.
Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da gidauniyar tare da fara rabar da littafan, Hon. Ibrahim Ali Usman ya sanar da cewa, akwai shirye-shiryen da gidauniyar ke da su na ganin ta taimaka wajen inganta harƙar ilimi da rage yawan yaran da ba su zuwa makarantar a shiryar Bauchi ta Kudu.
A cewarsa, ta hanyar taimaka wa ilimin yara za a samu nasarar rage yawan waɗanda ba su zuwa makaranta. Kazalika, ya ce, babban abun damuwa ne yadda yara ke gararanba ba tare da zuwa makaranta ba, don haka ne ya ce za su bada nasu gudunmawar wajen rage wannan matsalar.
Hon. Ali ya kuma shelanta cewar gidauniyar nasa na da babban burin taimaka wa rayuwar ‘ya’ya mata ta fuskoki daban-daban musamman a ɓangaren samar musu da ayyukan yi da kuma kula da iliminsu.
Sauran ɓangarorin da ya ce za su maida hankali a kai har da kula da rayuwar matasa domin ganin an rage yawan matasan da ba su da ayyukan yi a cikin al’umma. Sai kuma a cewarsa ɓangaren kiwon lafiya shi ma zai samu tagomashi a gidauniyar.
A faɗin shugaban gidauniyar: “Daidai gwargwado, daidai yadda ya sauwaƙa za mu cigaba da taimaka wa jama’a, za mu taimaka wa talakawa iyaka ƙarfinmu.
“A shirin mu na bunƙasa harkokin ilimi mun tsara cewa za mu biya wa mata da matasa kuɗin zana jarabawar kammala sakandari a ƙananan hukumomi bakwai da suke Bauchi ta Kudu.
“Ina yi wa mata albishir zan taimake su, kullum mafarki na ke yi kan rayuwar ‘ya mace, uwa-uwa. Iyaye mata, ƙannenmu mata, yayunmu mata Insha Allah za mu tallafa musu za mu taimaka musu daidai.
“Su kansu matasa za mu taimaka musu sosai, amma gaskiya gidauniyata za ta fi bada muhimmanci ne ga mata ds yara ƙanana da kuma marayu da marasa galihu,” ya tabbatar.
Shi kuma nasa ɓangaren, Alhaji Garba Abdu Garkuwan Kundum, ya ce, irin taimakon da Hon. Ibrahim Ali Usman ke bayarwa a ɓangarori daban-daban ba su misaltawa, don haka ne ya masa fatan cewa ya fito neman takarar Sanatan Bauchi ta Kudu.
“Tsawon lokaci bawan Allah din nan yana taimaka wa jama’a ta ɓangarori daban, kula da lafiya, sana’o’i, ilimi da sauran ɓangarori. Mutumin da yake irin wannan aikin alkairi kuma ba siyasa yake yi ba, in ya zama ɗan takara kuma Allah ya ba shi nasara jama’a za su ƙara cin gajiyarsa.
“Don haka muna masa kira da fatan ya fito neman takarar Sanatan Bauchi ta Kudu a zaɓen 2027 domin ya cigaba da ayyukan alkairin da yake yi. Ina da yaƙinin zai yi nasara kuma zai kyautata rayuwar jama’a. Irin waɗannan mutanen muke nema a cikin al’umma,” ya shaida.
Shi ma Hon. Bello Usama ya ce: “Muna son mu kara kwarin gwiwa ga shugaban wannan gidauniyar da ka sani duk lokacin da ka cigaba da taimaka wa mutane, Allah yana cikin taimakon ka ne.
“Ilimi shi ne mafarin ɗan adam duk wanda ya baka ilimi zai baka komai da ya mallaka a rayuwarsa. Za mu bi lungu da sako mu ranar da littafin nan domin yaran talakawa su samu damar yin karatu, wata rana kuma za mu nema musu guraben karatu da ɗaukan nauyinsu ne dukka ta cikin wannan shirin,” ya tabbatar.