HausaLatest

Harin Zabarmari: Buhari ya jajanta kan kisan manoma 43

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari ya bayyana alhinin yankan ragon da mayakan Boko Haram da yi wa wasu manoman shinkafa 43 a Zabarmari, Jihar Borno.

Mayakan sun far wa manoman su 60 da suka je kwadago a gonakin shinkafa a Zabarmari, Karamar Hukumar Jere, Jihar Borno suka yi musu kisan gilla.

“Ina Allahwadai da kisan da ’yan ta’addan suka yi wa hazikan manomanmu; daukacin Najeriya na alhinin wannan kisa na ba gaira babu dalili.https://d9477343bb13a124b58d57dc7a2121ec.safeframe.googlesyndication.com/safeframe/1-0-37/html/container.html

“Ina mika ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah Ya rahamshe su”, inji Buhari a sakon da ya fitar ta hannun kakakinsa, Garba Shehu a ranar Arar Asabar da dare.

Buhari ya kara da cewa gwamnati “na goyon bayan sojoji kuma tana ba su dukkannin gudunmuwa da suke bukata domin kare rayukan jama’ar Najeriya da ma kasar daga ‘yan ta’adda”.

Yadda abin ya faru

’Yan Boko Haram din sun daddaure manoman da suka je yin kwadago daga jihar Sakkwato, suka yi wa 43 yankan rago, suka jikkata shida wasu takwas kuma ba a san inda suke ba.

“Mun gano gawarwaki 43 da aka yi musu yankan rago da kuma wasu mutum shida da aka yi wa munanan raunika. “Ko tantama babu [aikin] Boko Haram ne da ke addabar yankin suna kai wa manoma hari”, inji shugaban kungiyar tsaron sa kai, Babakura Kolo.

Wani dan sa kai, Ibrahim Liman, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: “Manoma 60 ne aka dauka aikin girbin shinkafa a gonakin; an yi wa 43 yankan rago, shida kuma sun samu raunuka”.

Ya ce ana zargin ragowar mutum takwas da ba a gani ba maharan ne suka yi garkuwa da su.

Manlam Bunu, wani mazaunin yankin da aka yi akin neman manoman tare da shi, ya ce an kai gawarwarkin kauyen Zabarmari, inda za a yi musu sallar jana’iza ranar Lahadi.

Wasu majiyoyi na cewa manoman su 66 shida ne da suka hada da masu gwadago 9 daga Jihar Zamfara, 8 daga Sakkwato da kuma 7 daga Jihar Kebbi; sauran kuma ’yan jihar Borno ne.

Majiyar ta ce maharan na zargin manoman ne da ba wa sojoji bayanai a kan motsinsu a yankin da ke Arewa maso Gabashin Jihar Borno.

Harin Boko Haram kan manoma

Tun a watan Satumba jihar Borno ta fara mayar da mutanen da suka yi gudun hijira zuwa garuruwansu a wani shiri da take nufin kammalawa a karshen 2020.

Jihar ta fara yunkurin ne bayan ingantuwar tsaro a wasu yankuna da kuma kammala ginin gidajen tsugunar da mutanen da suka yi gudun hijirar a garuruwansu.

Gwamna Babagana Zulum ya ce jihar na fatan hakan zai ba wa mazauna yankunan damar ci gaba da harkokinsu na noma da sauran hadahadan tattalin arziki kamar yadda suka saba a baya.

A watan Oktoba mayakan Boko Haram sun kashe manoman rani 22 a wurare daban-daban a kusa da Maiduguri.

A baya-bayan nan, mayakan Boko Haram da ISWAP sun yawaita kai hare-hare a kan masu saran itace, makiyaya, manoma da masunta bisa zargin yi wa jami’an tsaro leken asiri.

ISWAP na da karfi a yankin Arewa maso Gabashin Jihar Borno inda lamarin ya auku.

Akalla mutum miliyan 2.7 ne hare-haren kungiyar Boko Haram ta tilasta wa yin gudun hijira a sassan jihar, inji Hukumar ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR).

Leave a Reply