Uncategorized

Gombe Ta Nemi Hadin Gwiwa Da Bankin Musulunci Don Bunkasa Zuba Jari A Bangarori Masu Zaman Kansu

Daga Khalid Idris Doya

A ci gaba da kokarin ta na janyo karin masu zuba hannun jari cikin jihar, Gwamnatin Jihar Gombe karkashin Gwama Muhammadu Inuwa Yahaya, ta tura tawaga ta musamman a taron Bankin Musulunci na shekara-shekara kan bangarori masu zaman kansu dake gudana a Birnin Jiddah na kasar Saudi Arebiya.

Tawagar ta Jihar Gombe dake karkashin Shugaban Kamfanin Zuba Jari da Bunƙasa Kadarori na Jiha Dakta Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) ta gana da tawagar jami’an bankin da suka hada da mataimakin shugaban bankin Dr. Mansur Mukhtar, da Manajan Bankin a Najeriya Dr. Ahsaru Kibria, da babban jami’in ofishin bankin a Nijeriya Mr. Mahmodou Alpha Bah da kuma jami’i a ofishin mataimakin shugaban bankin dake Jiddah Abdulkadir Baba-Ahmed.

Tattaunawa tsakanin tawagogin biyu ta fi maida hankali ne kan yadda shahararren bankin zai zuba kudi da kwarewarsa wajen dafawa gwamnatin Jihar Gombe a muhimman sassan bunkasa tattalin arziki. Sun kuma tattauna musamman kan yadda bankin zai shigo babban taron zuba jari na Jihar Gombe (Goinvest 2.0) karo na biyu gadan-gadan, biyo bayan nasarar taron na farko da aka yi a watan Disamban bara.

Tawagar ta Gombe ta kuma nemi tallafin Bankin na Musulunci game da cibiyar masana’antu ta Muhammadu Buhari, ta hannun Hukumar Bunkasa Zuba Jari ta Nijeriya don bankin ya halarci kaddamar da cibiyar masana’antun a hukumance da za a yi nan bada jimawa ba.

Cibiyar masana’antun dake Dadinkowa, dake da tazarar kilomita 40 daga Gombe babban birnin jihar, tana da girman kadada 1,000 wacce aka samarwa kayayyakin aiki dana more rayuwa kamar ruwa, hanyoyi da wutar lantarki, lamarin dake samar da kyakkywan yanayin aiki ga kamfanoni da masana’antu.

Game da shirin bashi maras kudin ruwa na Gombe kuwa da ake kira Gombe Green Sukuk, Bankin na Musulunci ya bada tabbacin bada cikakkiyar gudunmawarsa wajen tsara shirin dama cikakken aiwatar da shi.

A fagen noma ma, bankin ta karkashin tawagar sa na noma, zai tallafawa shirin bunkasa kiwo kai tsaye, da kafa cibiyar samar da magungunan cizon maciji a jihar don magance matsalar yawan saran maciji da sauran matsalolin kiwon lafiya ga al’ummar jihar.

Madatsar ruwar ta Balanga wato Balanga Dam, madatsar ruwa ta biyu mafi girma a jihar, ita ma za ta amfana daga hadin gwiwar. Za a aiwatar da aikin madatsar ruwan ne da cikakken tsarin kasuwanci da tsarin zuba jari don cin gajiyar alkairan dake tattare da madatsar don ci gaban Jihar Gombe

Shi ma gandun kiwo na Wawa-zange za a maida hankali akan sa yadda ya kamata. An amince cewa Jihar Gombe za ta marawa gidauniyar MercyCorps baya don gaggauta bunƙasa harkoki a gandun don amfanin al’ummar jihar.

Tawagar ta Bankin Musulunci ta bada tabbacin cewa bankin a shirye yake ya dafawa jihar a muhimman fannoni don bunkasa zuba jari da tallafi, tana mai bayyana kwarin guiwar cewa jihar ta nuna tabbacin cewa ita nagartacciyar kawa ce a fagen ci gaba.

A tawagar ta Jihar Gombe har da mai bai wa Gwamna Shawara na Musamman kan Kasafi, tsare-tsare da kula da hulda da abokan ci gaba Dr. Ishiyaku Mohammed, da Manajar Daraktan Kamfanin Onyx Consultant, Hajiya Aisha Bako.

Leave a Reply