Uncategorized

Gwamna Inuwa Jajirtaccene Akan Tabbatar Da Ci Gaban Jihar Gombe –Inji Daraktan Yada Labarai

Daga Idris Khalid
Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya bayyana cewa tun hawan Gwamna Inuwa kan karagar mulki ya kasance mai jajircewa da sadaukar da kai ga ayyukan ci gaban jihar Gombe.
A wata hira da aka yi da shi a yau Alhamis, Misilli ya ce yayin da wasu ke hankoron kashe kishirwarsu ta son mulki, Gwamna Inuwa ya shagaltu ne da gina kasa da kuma garambawul a sassa daban-daban na jihar domin fadada harkokin tattalin arziki da zamantakewa da samar da ayyukan yi.
“Yayin da wasu ke shirya wa shekarar 2023, shi kuwa mai girma Dan Maje yana ta kokarin kulla alaka ne da ma’aikatun gwamnatin tarayya da sauran ma’aikatun gwamnati domin lalubo hanyoyin hadin gwiwa don ciyar da Jihar Gombe gaba, burin sa shi ne ya yiwa al’ummar sa hidima ta hanyar data dace bawai ya ci amanar da suka dora masa ba. “Sanannen abu ne cewa Jihar Gombe tana baya wajen samun kason kudaden shiga mai tsoka daga asusun tarayya, amma sakamakon hazaka da jajircewarsa wajen ganin ya cika burin wadanda suka samar da jihar, a yan shekaru biyu da ya shafe akan karagar mulki, ya mayar da Gombe abin koyi wajen samar da kudaden shiga inda ta koma yin kafada da kafada da manyan jihohi.
Mai magana da yawun Gwamnan ya ce “Gombe insha Allahu, nan da wani lokaci, zata iya gudanar da harkokin ta ko da ba tare da kaso daga tarayya ba.”
Ya ce tun da aka kafa Jihar Gombe shekaru 25 da suka gabata galibin ma’aikatun jihar da sauran muhimman ofisoshin gwamnati suna watse ne a gine-ginen haya, amma saboda hangen nesa irin na Gwamna Inuwa, yanzu ya kammala shirye-shiryen gina sakatariyar data dace da jihar domin a samu sauki da kuma tafiyar da al’amuran mulki yadda ya kamata.
Mai magana da yawun Gwamnan yace, domin samar da makoma mai kyau da bukatun ‘yan kasa, Inuwa yana daukar matakan da suka dace don karfafawa da dorewar ci gaban tattalin arziki da bunkasa rayuwar al’ummah.
“Domin tabbatar da cewa matakan da aka dauka da kuma sakamakon da aka samu sun kasance yadda ya kamata kuma sun yi daidai da hangen nesa da manufofinsa, Gwamnan ya fito da wani tsari mai karfi, mai taken ‘Shirin ci gaban Jihar Gombe, ‘DEVAGOM’ don gina cibiyoyi masu karfi tare da dora jihar a kan turbar bunƙasa walwala da tattalin arziki mai dorewa”.

Leave a Reply