Uncategorized

Gwamnan Gombe Ya Taya Mai Alfarma Sarkin Musulmi Murna Bisa Cikarsa Shekaru 65 A Duniya

Daga Idris Shehu Zarge

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan na Sokoto kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku murnar cika shekaru 65 a duniya

A wani sakon taya murna da gwamnan ya buga a manyan jaridun kasar nan, Gwamna Inuwa ya bayyana Sultan Sa’ad a matsayin shugaba na gari da ya cancanci a yi koyi da shi.

Ya ce, “Kai shugaba ne na kwarai mai sadaukar da kai wajen hidimtawa wannar al’umma, kuma muna alfaharin yin cudanya da kai tare da zama abun koyi a gare mu.”

“Mai alfarma, mu anan Gombe muna alfahari da farin ciki bisa sadaukar da kai da kake yi ga bautar Allah da hidimtawa al’umma, dama irin muhimmiyar rawar da kake takawa wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin mabanbantan al’ummomin Nijeriya, dama rawar da kake takawa wajen ci gaban masarautun gargajiya da al’ummar Musulmi.”

A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, Gwamna Inuwa ya bi sahun sauran masu fatan alheri da taya murna wajen taya uban kasan murna, tare da addu’ar Allah ya kara masa lafiya da basira don ci gaba da samar da shugabanci abun koyi don kyautatuwar Nijeriya da al’ummar Musulmi da sauran jama’a baki daya.

Leave a Reply