Uncategorized

Gwamnatin Tarayya Ayyana Ranakun Laraba Da Alhamis Don Hutun Babbar Sallah

Daga Khalid Idris Doya

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba 28 ga watan Yuni da Alhamis 29 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutun Babbar Sallah.

Hakan na kunshe ne ta cikin sanarwar da babban Sakataren ma’aikatar kula da harkokin cikin gida, Oluwatoyin Akinlade ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutun Babbar Sallar Layya.”

Gwamnatin ta taya al’ummar musulmi a Nijeriya da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje murna bisa zagayowar Idin Layya tare da fatan za a yi bukukuwa cikin koshin lafiya.

“Muna fatan al’ummar musulmi za su addu’o’in a lokutan bukukuwan ga cigaban zaman lafiyar kasa da bunkasar ciki mai daurewa. Muna fatan a yi bukukuwa lafiya,” sanarwar ta ce.

Leave a Reply