Hausa

Harkar Musulunci Ta Kai Ƙarar Uba Sani, Kwamishinan Ƴan Sandan Kaduna Kan Kashe Masu Muzahara Bakwai

Daga Zailani Mustapha

Dandalin Resource Forum na Harkar Musulunci a Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky, ta kai ƙarar Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani da Kwamishinan ƴan Sandan jihar Mista Ali Audu Dabigi dangane da kisan gillar da suka yi wa mutum bakwai masu muzaharar lumana a Kaduna da Zariya.

Takardar koken mai kwanan watan 23 ga Afrilu, 2024, wadda wakilinmu ya gani, ta samu sa hannun Farfesa Abdullahi Danladi, shugaban Dandalin na Resource Forum, kuma an aika ta ne zuwa ofisoshin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, da kuma shugaban hukumar ‘yan sanda.

A ranar 30 ga watan Afrilu, 2024, ofisoshin waɗanda aka ambata suka karɓi takardar koken tare da kuma amincewa da koken.

Takardar koken na cewa; “Muna rubuta wannan wasiƙa zuwa ga ofishinku domin mu kusance ku bisa abin da Gwamnan jihar Kaduna da Kwamishinan ƴan sandan jihar Kaduna suka yi wanda bisa umurnin su ne ƴan sandan Nijeriya suka buɗe wa masu muzaharar goyon bayan Falasɗinawa a Kaduna da Zariya wuta a ranar 5 ga Afrilu, 2024 da harsashi mai rai.”

Koken ya ƙara da cewa; “Rikicin Gabas ta tsakiya tsakanin Falasɗinu da Isra’ila wani lamari ne da ya shafi duniya wanda ya mamaye ta ya kuma ɗauke ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya tun daga watan Oktoban 2023. Wannan lamarin ya haifar da zanga-zangar nuna adawa da kisan gillar da sojojin tsaron Isra’ila ke yi wa fararen hula marasa laifi a Zirin Gaza. Ana ci gaba da tafka zanga-zangar ba tare da tsayawa ba a Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus da sauran ƙasashen Turai ciki har da ita kanta Isra’ila. A Nijeriya ana ci gaba da gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi da dama da suka haɗa da Kaduna da Kano da Legas da Ribas da kuma babban birnin tarayya Abuja.

“An sanya ranar Juma’ar ƙarshe ta watan Ramadan a matsayin ranar Ƙudus ta duniya kuma ana gudanar da ita ne a faɗin duniya. An shafe shekaru 40 ana gudanar da taron a Nijeriya. An yi bikin ranar Qudus ta duniya a wannan shekara a duk duniya a ranar 5 ga Afrilu 2024 ciki har da Nijeriya inda aka yi muzaharori a fiye da birane 30 da suka haɗa da Kaduna da Zariya.

“Dukkanin jerin gwanon da aka yi a duk jihohin an gudanar da shi ba tare da wata matsala ba, an kuma yi shi lafiya a ko’ina ciki har da Legas, Ribas da Abuja. Sai dai abin takaicin shi ne kwamishinan ƴan sandan jihar Kaduna ya yanke shawarar yin amfani da ƙarfinsa inda ya kai hari a kan muzaharar lumanan. A sakamakon haka, ya umurci ‘yan sandan da su buɗe wuta da harsasai masu rai da rana tsaka kan masu muzaharar ta lumana da ba su ɗauke da makami. Wannan ya kai ga kashe mutane 7,” in ji koken.

“Muna ganin abin da Gwamnan jihar Kaduna da Kwamishinan ƴan sandan jihar Kaduna suka yi a matsayin son rai, wanda kuma ya saɓa wa kundin tsarin mulki, sannan kuma ya saɓa wa ƙa’idojin aikin ƴan sandan Nijeriya. Kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya ya yi tanadi da kuma kare haƙƙin kowanne ɗan Nijeriya wanda ya haɗa da ‘yancin rayuwa, ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana da dai sauransu. Idan aka bar ayyukan waɗannan mutane biyun, kimar Nijeriya za ta zube a idon ‘yan ƙasa da sauran ƙasashen duniya.

“A bisa haka ne muka miƙa muku wannan koke domin ɗaukar matakin da ya dace kan Gwamnan jihar Kaduna da Kwamishinan ƴan sanda Mista Ali Audu Dabigi kan take haƙƙin ‘yan ƙasa. A yayin da muke sa ran za ku mayar da martani cikin gaggawa, muna yi muku fatan alheri a cikin ƙoƙarinku, ”in ji ƙarar.

Leave a Reply