Uncategorized

Kirisimeti Da Sabuwar Shekara: NIS Za Ta Kafa Cibiyoyin Yin Fasfo Ga Mazauna Ketare


Shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), Isah Jere Idris ya umarci a gaggauta samar da cibiyoyin yin Fasfo ga mazauna kasashen waje a dukkanin filayen Jirgin sama na kasa da kasa domin saukaka wa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje saukin samun Fasfo domin su samu zarafin dawowa domin halartar bukukuwan Kirisimeti da na sabuwar shekara cikin annashuwa.


A wata sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar ta NIS Anthony Akuneme ya fitar a Abuja, ya ce, kwanturola Janar din ya kuma bada umarnin cewa ofisoshin da ke kula da aikin Fasfo da su Kara Bada fifiko ga ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje da iyalansu lura da cewa su din suna da takaitaccen lokacin komawa zuwa kasashen da suke rayuwa a can. 


Ya ce, “CGIS ya nanata himmar hukumar na cigaba da yin aiki tukuru ga ‘yan Nijeriya da suke zaune a cikin kasa da katare, tare da ma wadanda ba ‘yan Nijeriya ba da suke sha’awar aikinmu.”


Kokarin hukumar na saukaka wa jama’a samun Fasfo cikin sauki a yayin wannan bukukuwan ya fara kankama ne tun makonnin da suka gabata a ofishin yin Fasfo na hukumar da ke sassan daban-daban na kasar nan domin har a ranakun karshen mako suna aikin Samar da Fasfo. 

Leave a Reply