Uncategorized

KUNGIYAR ‘ZADAWA YOUTHs FORUM’ SUN KARRAMA HON. BAKOJI ALIYU BOBBO DA LAMBAR YABO

.Daga : Mohammed kaka Misau, Bauchi.
Kungiyar Zauren Matasan Zadawa dake karamar hukumar Misau sun karrama Hon. Bakoji Aliyu Bobbo shugaban marasa rinjaye a majalisa da lambar yabo bisa kokari da jajircewa gurin cigaban al’ummar yankin Chiroma da jihar Bauchi baki daya.

Shugaban wannan kungiya, Mal. Salisu Waziri Zadawa da wasu daga cikin mukarraben wannan kungiya ne suka Mika wannan lambar yabo mai taken ” Award of Merit For Your Utmost Commitments and Contributions for the Development Of Chiroma Constituency and Bauchi State at Large” wa shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Bauchi.

Yayin Mika wannan kyauta tawagar sun bayyana Jin dadin su bisa kokari da Hon. Bakoji Aliyu Bobbo keyi yau da kullum gurin shiga cikin hidimar al’ummah a matsayin Gwarzon wakili mai kokari da himma gurin kawo cigaba wa al’ummah.

Anashi jawabin, Hon. Bakoji Aliyu Bobbo yayi godiya bisa wannan karramawa tare da nuna Jin dadin sa kan lambar yabo da wannan kungiyar ta bashi a matsayin sa na wakili kuma Mai ruwa da tsaki a harkar siyasa a karamar hukumar Misau.

Shugaban marasa rinjaye ya bayyana wannan kungiya a matsayin kungiya ta farko da ta fara zawarcin sa kan ya fito kujerar MISAU/DAMBAM don su bashi gudumawa daga yankin su kwanakin baya.

Akan wannan batu ya kara bayyana cewa “Jam’iyyar PDP Jam’iyya ce mai Da’a da tsari wanda dukkan wanda ke ciki yasan haka, saboda haka dukkan abunda Jam’iyya da masu ruwa da tsaki na PDP suka ce shine abun da za’ayi kan kowani matsayi.

Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar hukumar Misau, Hon. Abdu Haruna Shima ya bayyana farin cikin sa tare da yaba wa wannan kungiya bisa lura da suka yi Kan abubuwan alkhairi da Hon. Bakoji Aliyu Bobbo keyi har suka taso takanas daga yankin su don nuna masa karamci, wannan abun a yaba ne. – Inji Chairman.

Daga karshe yayi addu’ar Allah ya saka da alkhairi, ya kara Zumunci a tsakani.

Leave a Reply