Uncategorized

Luguden Wuta Kan ‘Yan Bindiga Ya Janyo Mutuwar Mutanen Gari 68 A Zamfara

Daga Hussaini Yero, Gusau

A kokarin da rundunar Sojojin sama ke yi na yaki da ‘yan bindiga a yankin Dansadau cikin karamar hukumar Maru cikin jihar Zamfara, mutanen gari sittin da takwas (68) wadanda galibinsu ‘yan kasuwar Muntunji ne sun rigamu gidan gaskiya sakamakon ruwan bama-bamai na kan-mai-uwa da wabi da sojoji suka yi a ranar Asabar.

Bayanai sun zo kan cewa lamarin ya faru ne sakamakon tserewa da ‘yan bindiga suka yi daga maboyarsu inda suka nufi cikin kasuwar Muntunji inda suka gwamutsu da mutanen garin kana kuma sojoji suka sako bama-bamai wanda a sanadiyyar hakan mutanen gari 68 suka mutu wasu karin mutum 38 kuma na kwance a asibitin Dansadau da Yarima Bakura da ke Gusau.

Wani ganau mai suna Sa’idu Isyaku Mutunji, ya shaida wa ‘yan jarida cewa, “Muna cikin kasuwa kwatsam sai mu ka ga ‘yan bindiga sun shigo cikin kasuwar a guje, ashe sojojin sama ne suka fatattako su daga can maboyarsu. Muna cikin kasuwar tamu ta Mutunji sai kawai muka ji ruwan bama-bamai na tashi.

“Kafin a ce kwabo mutane na ta faduwa wasu sassan jikin su babushi kasuwar ta turnike da hayaki sai gawarwaki muke gani da mutane kwace da raunuka wasu babu sassan jiki,” in ji Saidu Mutunji.

Sa’idu ya cigaba da tabbatar da cewa, “Ya zuwa jiya Lahadi mun yi jana’izar mutane 68 a garin Mutunji, kuma yanzu haka ga shi mun kawo mutane sha biyu asibitin Yariman Bakura ashirin da takwas na Asibitin Dansadau.”

Kwamishinan tsaro na jihar Zamfara, Maman Tsafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa, “Sakamakon hari da Sojojin sama su ka kai wa ‘yan bindinga ya yi sanadiyar mutawar mutane da dama wandada har zuwa yanzu bamu gama sanin adadinsu ba. Adadin wadanda aka kashe da wadanda aka jikkata muna kan bincike zuwa yanzu mu tantance adadin,” ya shaida.

Haka kazalika ‘yan jaridu sun ga gawarwakin Sojojin goma a asibiti Yariman Bakura wadanda aka taho da su daga Mutunji. Sannan zuwa yanzu ba san adadin ‘yan bindiga nawa ne suka mutu a wannan harin da sojojin suka kaddamar ba.

Ya zuwa aiko da wannan labarin rundunar Sojojin sama ba ta fitar da wani sanarwa kan wannan lamarin ba.

Leave a Reply