Uncategorized

MAAUN Nijar Ta Jajantawa Iyayen Dalibinta, Bashir Muhammad Sani Bisa Rasuwarsa


Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), dake Maradi, ta jajantawa iyayen dalibin jami’ar, Bashir Muhammad Sani, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 7 ga watan Agusta, 2022 sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Kano zuwa Bauchi.


Kafin rasuwarsa, Marigayin ya kasance yana matakin aji na 400 a jami’ar inda yake karantar ilimin zamantakewa.


Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban MAAUN Nijar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu da kansa, kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Lahadi.


Hukumar gudanarwa ta MAAUN ta bayyana rasuwar dalibin a matsayin babban rashi ba kawai ga iyayensa da ‘yan uwansa ba har ma da daukacin ma’aikata da daliban jami’ar.
Shugaban MAAUN din har wala yau ya kuma bayyana Marigayin a matsayin dalibi mai kwazo da tarbiyya mai mutunta Dattijai da sauran al’umma musamman Malamansa.


“A madadin hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijar, ina mika ta’aziyyarmu ga iyaye da ‘yan’uwa da abokan marigayin.


“Mahukumtan jami’ar na kuma mika ta’aziyya ga gwamnatin Jamhuriyyar Nijar da daliban jami’ar bisa rasuwar Bashir Mohammed Sani, Allah ta’ala ya gafarta masa kurakuransa,” in ji Farfesa Abubakar Gwarzo.


Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya jikan Marigayin ya sanya shi a Aljannar Firdaus, ya kuma bai wa iyayensa da ‘yan’uwa hakurin jure rashin nan da ba za a iya maida shi ba.


Za a yi jana’izar Mohammad Sani a ranar Litinin (Gobe) a mahaifarsa ta Bauchi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Allah ya jikansa da rahama, ameen.

Leave a Reply