Uncategorized

Mun Dauki Kwararan Matakan Dakile Cutar Kwalara A Gombe, Inji Gwamna Inuwa

Daga Idris Shehu Zarge

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya shaida cewar, gwamnatinsa, tana kan yin aikin hadaka da cibiyar kula da cututtuka ta kasa wato (NCDC) wajen kare jihar daga annobar Kwalara da kuma ta Kwarona Bairus wanda ya misalta hakan a matsayin kyakkyawar matakin da ke taimaka musu wajen kula da kiwon lafiya a halin yanzu.

Malam Inuwa da ke amsa tambayoyin ‘yan jarida jim kadan bayan ganawa da shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa a jiya kamar yadda Ismaila Uba Misilli , Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnansa ya nakalto mana.

A cewar gwamnan: “Gombe ta kasance mai kwazo kuma muna hadin gwiwa da NCDC tun farko. Ya zuwa ranar 20 ga watan Maris na 2020 tuni mun riga mun kafa kwamitin aiki da cikawa dake kula da cutar wadda Farfesa Idris Mohammed ya jagoranta. Bisa hakan mun samu damar kula da cutar yadda ya kamata. Dangane da cutar kwalara kuwa Gombe tana cikin jihohin da suka samu bullar cutar kwanan nan, amma mun rage yawan kamuwan, saboda ba tare da bata lokaci ba muka samu nasarar shawo kan yaduwar ta kuma yanzu Gombe ta fita daga wannan lamarin,” in ji shi.

Dangane da lambar yabo da aka baiwa Gombe kwanan nan a matsayin jihar da ta yi zarra a saukaka harkokin kasuwanci, Gwamnan ya ce jihar za ta ci gaba da tallafawa harkokin kasuwanci da sauran fannoni.

“Mun fahimci cewa don kasuwanci ya bunƙasa, dole ne a saukaka da bayar da isasshen tallafi ta kowane fanni, da suka hada da tsaro, da kiwon lafiya, da ilimi, da kwarewa da habaka kasuwanci, wanda mutanen mu suka shiga ciki. Kasancewar mu manoma ne, mun karfafa jama’ar mu da su tsunduma cikin harkar noma da sarrafa albarkatun gona.

“Wannan shine dalilin da yasa muke da ayyukan kasuwanci da dama kuma hakan ya kaimu matsayin na ɗaya sakamakon waɗannan abubuwan da muka samu damar kulawa da su, ”in ji Gwamnan.

Bugu da kari, ya ce an kammala tabbatar da sansanin masana’antu kuma za a bayar da aikin sa a karshen wannan watan, ya kara da cewa aikin, wanda ya kai kadada 347 na fili zai lashe kudi Naira biliyan 17.

Game da abubuwan da ke faruwa a halin yanzu a cikin jam’iyyar APC kuwa, Gwamna Inuwa ya ce: “Ban yarda cewa jam’iyyar mu na cikin rikici ba. Siyasa kamar kowane fanni na rayuwar ɗan adam tana da matsaloli da yawa kuma ina tsammanin kwamitin rikon yana tafiyar da jam’iyyar yadda ya kamata cikin inganci.”

Kan harkar tsaro kuwa, gwamna Inuwa, ya bayyana cewar dukkanin matakan da suka dace wajen kiyaye jihar da inganta tsaro suna dauka wanda hakan ke taimaka musu wajen kare duniya da rayukan al’umman jihar.

Leave a Reply