Uncategorized

NIMASA Ta Agaza Wa ‘Yan Gudun Hijira Da Kayan Sana’o’i A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya

Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa a Nijeriya ‘Nigerian Maritime Administration and Safety Agency’ (NIMASA) ta baiwa gidauniyar Ambasada Yusuf Maitama Tuggar tallafin kayayyakin sana’o’in hannu domin rabawa ga ‘yan gudun hijira, gajiyayyu da marasa galihu a Jihar Bauchi.

Da ya ke mika kayan ga gidauniyar, Musa Adamu wanda ya jagoranci jigilar kayan a madadin NMASA, ya shaida cewar manufar bada tallafin domin taimaka wa rayuwar ‘yan gudun hijira da kuma jama’an da suke cikin kuncin rayuwa da marasa galihu a cikin al’umma domin rage musu kaifin kalubalen rayuwa da suke fuskanta.

Ya bayyana cewar jihohi da dama suna cin gajiyar shirye-shiryen hukumar, inda ya nemi wadanda za a baiwa tallafin da su tabbatar da yin amfani da su ta hanyoyin da suka dace domin taimakawa rayuwarsu a kowani lokaci.

Da ya ke amsar kayayyan a ofishin gidauniyar da ke Bauchi, Alhaji Bello Muhammad Tukura, ya bayyana cewar za su tabbatar da yin rabon cikin gaskiya da adalci, inda yake mai cewa su kansu a gidauniyar sukan sayo kayayyaki domin rabar wa jama’an da suke fama da yanayin rayuwa, don haka ne ya nuna cewa wannan tallafin karfafawa ne ga aikace-aikacen nasu.

Tukura, ya jero tallafin kayan da suka amsa da cewa kekunan dinki guda 12, Injinan nika na markade guda 12, Injunan walda guda 12, na’urar yin aski tare da dukkanin kayansa guda 50, Janaretoci guda 12, mashin mai kaafa uku (Keke-Napep) guda 2, da kuma Injunan ban-ruwa na noma guda 10.

“Sun kawo tallafin domin mu raba wa marayu, gajiyayyu da ‘yan gudun hijira domin su gudanar da sana’o’in hannu don inganta rayuwarsu.

“Hatta mu a wannan gidauniyar aikin da ke gabanmu a kowani lokaci taimakawa gajiyayyu mukan sayo kayayyaki domin raba musu. Balle kuma da muka samu tallafi don haka wannan yana kara tabbatar da cewa aikinmu na samun karbuwa da inganci.”

Ya nuna godiyarsu ga hukumar tare da cewa za su tabbatar da yin rabon ga wadanda aka bada tallafin dominsu ba tare da nuna son kai ba, ya kuma yi fatan za su kara samun wasu nau’in kayayyakin domin cigaba da taimaka wa jama’a musamman talakawa a ciki da wajen jihar Bauchi.

Ya ce, nan kusa kadan za su rabar da kayan ga wadanda Allah ya sa za su ci gajiyarsu da zarar suka kammala tsare-tsare da shirye-shiryen wannan rabiyar.

Leave a Reply