NYSC Ta Karyata Shirin Tura ‘Yan Hidima Wa Kasa Fafata Yaki A Nijar
Daga Khalid Idris Doya
Hukumar Kula da Matasa Masu Hidima Wa Kasa (NYSC) ta karyata labarin da ke zargin cewa da yiyuwar gwamnatin Nijeriya za ta tura mata masu hidima wa kasa zuwa Jamhuriyyar Nijar domin fafata yaki a kokarin dawo da mulkin demukuradiyya.
Daraktan yada labarai na hukumar NYSC, Eddy Megwa, ya shaida ta cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Asabar, tare da misalta rahotonnin a matsayin na kanzon kurege.
Ya bukaci al’umma, musamman matasan da ke kan hidimta wa kasa, masu shirin shiga hidima wa kasa, da iyayensu da su yi watsi da rahoton da wasu masu kokarin kawo rudani suka kirkira.
Sanarwar ta ce, “Hankulanmu sun karkata kan wani faifayin bidiyo da ke yawo a kafafen sanarwar zamani da ke zargin cewa gwamnatin tarayya za ta iya tura mambobin da ke hidima wa kasa zuwa jamhuriyyar Nijar domin fafata yaki domin farfado da mulkin demukuradiyya a can.
“Kai tsaye mu na shaida cewa labarin babu gaskiya kwata-kwata a ciki, kagegge ne da wani ya kirkira domin ya samu masu ziyararta shafinsa.”
Daga bisani hukumar ta gargadi wadanda suka kirkira labarin da su gaggauta dainawa tare da daina yada hakan domin zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasa.
Sanarwar ta ce, hukumomin tsaro za su tabbatar da dakile masu yada labarin na bogi.