Uncategorized

Ra’ayin Harsashen Bayan Mulkin Buhari Ga Arewa Da ‘Yan Arewa

Ra’ayin Aliyu Dahiru Aliyu

Ku rubuta ku ajiye, mulki zai bar Arewa ya koma Kudu bayan Buhari ya gama nasa. A wannan lokacin yan siyasar da basu tsinananawa Arewar komai ba za su fara neman guraben mukamai a sabuwar gwamnati amma ba za su samu ba. Daga nan za su fara cewa ana shirin karya Arewa ko rusa Musulinci.
Hare-haren yan ta’adda da garkuwa da mutane za su ci gaba. Malaman da suke gaya mana cewa kashe-kashen da ake mana a yanzu kaddara ce ko zunubanmu ne, su ne za su fito su ce ana shirin rusa musulinci ne a Najeriya saboda shugaban kasa ba musulmi ba ne.
Daga nan yan kishin Arewa na karya da suke nufin komai a bawa Arewar shi ne ci gaba za su sake fitowa. Za su manta duk wasu manyan mukamai Buhari yan Arewar ya bawa amma ba su yi mana komai ba, sai a lokacin za su dinga cewa ana nisantar da Arewa daga mulkin Najeriya.
Abin da za ka yi la’akari a ko da yaushe shi ne, idan dan siyasa ya ce maka Arewa to yana nufin shi da abokansa da za su samu kudin gwamnati ko da dukanmu za mu mutu a talauci. Idan malamin addini ya ce maka yana kishin musulinci to yana nufin abin da zai samu a gurin shugabanni a ofisoshi idan su musulmi ne.
Da yan siyasa da yan kasuwar addini sun hada kai guri guda suna taimakekeniya wajen rusa talaka. Shi kuma ya siyar da kwakwalwarsa ana hadashi rigima da dan uwansa. An bautar da tunaninsa ta yadda yake tsoron mai nemar masa yanci fiye da wanda yake bautar da shi.

Leave a Reply