Uncategorized

Tsohon Daraktan Yakin Zaben Tsohon Gwamnan Bauchi, Ya Koma Labour Party

Daga Khalid Idris Doya

Tsohon daraktan yakin zaben tsohon gwamnan jihar Bauchi, Muhammadu Abdullahi Abubakar, Alhaji Garba Sarki Akuyam ya shelanta ficewa daga jam’iyyar APC tare komawa cikin jam’iyyar Labour Pary (LP) tare da daruruwan magoya bayansa.

Akuyam wanda tsohon kwamishinan kudi da cigaban tatttalin arziki na jihar Bauchi ne, ya shelanta komawa LP ne a ziyarar da ya kai wa shugaban jam’iyyar a jihar Bauchi, Barista Hussaini Saraki a ofishin jam’iyyar jiya, yana mai cewa, ya tuntubi masu ruwa da tsaki da magoya bayansa kafin daukan wannan matakin.

Akuyam ya bayyana cewar dalilansa na ficewa daga cikin APC sun hada har da rashin gamsuwarsa da yadda ake gudanar da lamura a cikin jam’iyyar a matakin jiha da ma kasa, kana ya bibiyi tarihin Peter Obi da irin nasarorin da ya cimma a rayuwarsa, don haka yana da kwarin guiwar Peter zai iya shawo kan matsalolin da suke addabar kasar nan.

Ya kara da cewa a matsayinsa na wanda ya ke da gogewa a bangaren siyasa da ya jagoranci jam’iyyar APC har ta kai ga samun nasara a zaben 2015 da ya gudana a jihar Bauchi, bai gamsu da yadda ake tafiyar da lamura a cikin jam’iyyar a halin yanzu ba, don haka ne shi da daruruwan magoya bayansa suka fice daga cikin jam’iyyar.

Ya kuma kara da cewa, abokin takarar Peter, Yusuf Datti Baba Ahmed, ya fito daga sannanen zuri’a a arewa kuma yana da kyakkyawar alaka da su don haka ne ya ga dacewar ya koma cikin jam’iyyar LP domin bada tashi gudunmawar wajen ganin sun samu nasarar lashe zabukan da ke tafe.

Kana Garba Sarki Akuyam tsohon kwamishinan bunkasa yankunan karkara na jihar Bauchi ne, ya bada tabbacin cewa zai yi dukkanin mai yiyuwa domin ganin nasarar jam’iyyar a dukkanin matakai, ya kuma nemi alfarmar jagorirn jam’iyyar da su amince da shi hannu biyu-biyu.

A jawabinsa na maraba, shugaban jam’iyyar Labour Party a jihar Bauchi, Barista Hussaini Saraki, ya shaida cewar wannan babban nasarace a garesu kuma yana mai bai wa Akuyam da sauran magoya bayansa tabbacin samun adalci a jam’iyyar.

“Tabbas samun kwararren masanin siyasa kuma masanin tattalin arziki a cikin jam’iyyarmu babban nasara ce a garemu. Sannan, yadda jama’a suke tururuwar shigowa cikin LP a jihar Bauchi na nuna mana irin gagarumar nasarar da za mu iya samu a zaben da ke tafe.”

Ya kuma nuna kwarin guiwarsa na samun nasarar jam’iyyar a dukkanin matakai, yana mai kira ga sauran jama’a da su shigo a dama da su domin ceto kasar nan daga halin da take ciki.

Saraki daga bisani ya jinjina wa Sarkin Akuyam bisa daukan wannan matakin da ya ce ya fi dacewa domin hada karfi da karfe wajen ceto Nijeriya.

Leave a Reply