Uncategorized

Yakin Rasha Da Ukraine Ya Janyo Gwamnatin Nijeriya Ba Za Ta Iya Karasa Aikin Karafa Na Ajeokuta Kafin Karewar Wa’adinta Ba

Gwamnatin tarayya ta ce, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba za ya iya kammala aikin sarrafa karafa na Ajaokuta da ake cigaba da yi a halin yanzu ba, kamar yadda ta yi alkawarin kammalawa a shekarar 2022 tun da farko.

 

Ministan ma’aikatar Tama da Karafa, Olamilekan Adegbite, shine ya shaida hakan a jiya lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa, ya bayyana cewar yakin da Rasha ta yi da Ukraine gami da kalubalen da aka fuskanta na annobar Korona ya janyo gwamnatin Nijeriya ba za ta iya cimma manufar da ta sanya a gaba ba.

Leave a Reply