Zababben Dan Majalisar Jama’are/Itas Gadau Ya Taya Musulmai Murnar Sallah, Ya Horesu Kan Dabba’a Koyarwar Ramadana
Daga Mohammed Kaka
Zababben dan majalisar wakilai Mai Wakiltar mazabar Jama’are/Itas Gadau daga jihar Bauchi Hon. Bala Rabiru Kashuri ya taya al’ummar musulmai murnar kammala ibadar watan Azumi lafiya tare da nemansu da kada su yi sako-sako wajen dabbaka koyarwar da suka yi a cikin watan na Ramadana.
A sakon da ya aike wa al’ummar musulmai a mazabarsa, Kashuri ya nuna cewa yadda aka fara azumin 1444/2023 aka kammala lafiya abun godiya ne ga Allah Madaukakin Sarki.
“Ina amfani da wannan damar wajen in taya duk al’ummar musulmai murnar sallah karama kuma ina fatan a gama shagulan bikin sallar lafiya ba tare da wani tashin hankali ba.”
Daga bisani ya nemi al’ummar kasa da su cigaba da gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya, cigaban kasa, da dauwamar kwanciyar hankali a tsakanin al’umma. Kana ya ce, zababbun shugabanni suna matukar bukatar addu’o’i domin sauke nauyin da ke kansu yadda ya dace.
Ya kuma yi addu’ar Allah maimaita mana na badin badada.