Uncategorized

Zaben Gomnan Bauchi: Jiga jigan Jam’iyyar APC sun mara baya wa tafiyar Air Marshal Sadiq.

Daga; Mohammed kaka Misau, Bauchi.

Gabannin babban zaben 2023 dake tafe, wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Bauchi Hon Sulaiman Bala Gumau ya bayyana goyon bayarsa na tsayawa takaran gomnan jihar Bauchi akan tsohon shugaban hafsan rundunar sojin saman Nigeria Air Marshall Sadiq Baba Abubakar.

Bala Gumau ya bayyana hakanne a yayin wata tattaunawa ta musamman da wakilinmu a jiya, inda ya bayyana tsohon hafsan rundunar sojin a matsayin wanda sunansa yayi shura a kowacce gida a jihar Bauchi a sakamakon shugabanci na baya ya sanya Al’umar jihar Bauchi ke masa kiranye daya tsaya takaran gomnan jihar Bauchi.

Gumau wanda ya kasance tsohon mai tallafawa gomna a bangaren tallafawa Al’uma a jihar Bauchi yace, ya fara shiga harkar siyasa ne tun a shekarata 1999, inda ya Kara da cewa ya kuma tsaya takaran shugabancin Karamar hukumar Toro a shekarata 2008 saidai bai samu nasara ba a wancan lokacin.

” Alokacin Mulkin Malam Isa Yuguda ya nadani mai tallafa masa a bangaren shirin yaki da talauci ta NAPEP kafin daga bisani na tsaya takaran dan Majalisar Lame a shekarata 2014 wanda anan ma ban samu nasara ba, kuma tun a wancan lokacin nake hidimar siyasa har zuwa wannan lokaci, kuma zamu bada dukkanin goyon bayan mu wa Air Marshall Sadiq Baba Abubakar a karkashin inuwar Jam’iyyar APC domin ya zamto gomnan jihar Bauchi a shekarata 2023 “, Acewarsa.

Bala Gumau yace tsohon hafsan rundunar sojin saman Nigeria a lokacin da yake rike da mukamin babban hafsan saman soji ya taka rawar gani wajen kawo Ayyukan cigaba a jihar Bauchi.

Acewarsa, dan takarar tasu bashida sha’awar shiga hidimar siyasa har sai bayanda Al’umar jihar Bauchi suka fara mishi kiranye daya fito domin neman takaran gomnan jihar Bauchi.

” Kirada Al’uman jihar Bauchi ke masa daya fito takaran gomnan jihar Bauchi baya rasa nasaba da irin dubban nasarori daya cimma a lokacin da yake aiki da rundunar sojin saman Nigeria harma zuwa lokacin da yayi ritaya daga aiki ” Acewar Gumau.

Jigon na jam’iyyar APC ya kuma bayyana cewa tsohon shugaban hafsan rundunar sojin saman Nigeria yana taimakawa Al’uma da dama wannan nema ya sanya yake samun nasara akan duk Abunda ya sanya a gaba.

Ya kuma zayyano Wasu daga cikin irin ayyuka daya Gudanar da suka hada da samarda filin tashi da saukan jiragen sama na rundunar soji, harma da samarda asibitin rundunar soji wanda yace shine na daya a fadin kasar nan baki daya.

“Ya kuma taimaki ‘yayan jihar Bauchi da dama ta hanyar samar musu da aiki a rundunar sojin saman Nigeria. Har ilayau ya kuma taimaka wajen ganin an samarda jami’an rundunar sojin saman Nigeria wanda tuni aka kammala ginashi kuma ana saran zai fara aiki nan bada dadewa ba, harma da sauran Ayyukan cigaba daya aiwatar”.

Daga karshe Sulaiman Bala Gumau yayi kiraga daukacin al’uman jihar Bauchi dasuyi taka tsantsan tareda yin nazari kan Mutanen kirki da zasu zaba wanda zasu musu ayyukan cigaba a yayin zaben da za’a Gudanar a shekarata 2023, ba wai wadanda zasu da zaran sun hau kan karagal mulki zasu manta dasu ba.

Leave a Reply