2023: Abdul Ningi ya bayyana Aniyar sa ta tsayawa takarar sanata a Bauchi ta tsakiya.

By: Anas Ado Saeed

Tsohon jagora a majalisar wakilai ta kasa sanata Abdul Ahmed Ningi ya bayyana Aniyar sa ta tsayawa takarar kujerar sanata ta Bauchi ta tsakiya a zabe Mai zuwa na shekara ta Dubu biyu da Ashirin da Uku.

Abdul Ahmed Ningi wada ya taba zamowa sanata a shekara ta 2011 zuwa 2015 ya bayyana Aniyar tasa ce wa masu ruwa da tsaki na Bauchi ta tsakiya karkashin jam’iyyar PDP a ranar 9/04/2022 a dakin taro na Command guest House dake Bauchi.

Abdul Ningi ya fadawa Masu ruwa da tsakin cewa “Na kirawo kune a yau domin ku sheda abinda na sheda, iuji abinda naji domin jam’iyyata ta PDP batta da ta biyu a gareni”.

Sanatan Wanda yace a halin yanzu sun kammala shiri tsaf domin tsayawa takarar, a cewar sa domin kare muradun ba iya Al’ummar Bauchi ta tsakiya kadai ba, dukkan Al’ummar Arewacin Najeriya baki daya.

Ya kara da cewa “Sama da shekara biyu mutane na tuntubata domin nayi takarar Amma Ina zillewa, na tsaya takara har sau tara Kuma nayi nasara sau bakwai”

Sanata Abdul Ningi yace kiranye da Al’ummar Yankin nasa ke masa, ya biyo bayan irin kyakykyawan jagoranci ne da sukace ya musu sunji dadi a lokacin da ya taba wakiltar su a baya.

Abdul yace “Yanzu mutane na suna mun kiranye na sake wakiltar sua matsayin sanata. Lallai mutane a Bauchi basa ce ba’ayi aiki ba, sai dai suce ba’a raba kudi ba”.

Ya kara da cewa “Gwamnan Bauchi ya nemeni mun iuma zauna dashi, ya bukaci na tsaya takarar sanata, shi kuma a tasa gudumawar zai Gina mun hanyoyi wa Al’ummar yankina na Miya zuwa Soro a karamar hukumar Ganjuwa, Bura zuwa Ningi a karamar hukumar Ningi da wassu sauran Wuraren, Kuma da jin haka na amince”

Yace ” zanyi alfahari matuka ida shugaban kasar Najeriya ya fito a yanki na na Arewa maso Gabas a shekara ta 2023, Kuma zabina shine Atiku Abubakar, duk da dai Gwabna Bala Muhammad ya nuna aniyar sa, Atiku shine zabina, Ina San su dukkan su duk Wanda Allah ya bashi abin Alfahari ne a gareni”, a cewar Abdul Ahmed Ningi.

Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan Ma’aikatar Yada labarai na jihar Bauchi Uon. Dayyabu chiroma, ya nuna godiyar sa wa Gwamna Bala Muhammad bisa jajircewar sa wajen ganin ya dawo da martabar Jam’iyyar PDP a jihar Bauchi.

Chiroma Wanda yace samun nasarar zabe ba abine me sauki ba, ya bukaci a nemi hadin kan Masu kada kuri’a kafin lokacin zaben.

Kwamishinan ya bukaci Uwar Jam’iyyar PDP data kara hubbasa wajen ganin ta cire kitse a wuta.

Da yake jawabi a wajen taron, Hon. Baffa Aliyu Misau yace, sanata Abdul Ahmed Ningi mutum ne na iwarai Wanda Al’umma sun gwada shi Kuma ya gudanar da kyakykyawan jagoranci, sannan ya Samar da ababen romon dimokuradiyya wa Al’ummar mazabar sa.

“Nayi niyyar tsayawa takarar kujerar sanata amma tunda na samu labarin cewa sanata Abdul Ahmed Ningi zai nemi wannan kujerar sai na hakura. Zamu hada karfi da karfe domin tabbatar da cewa munyi nasara a zaben shekara ta 2023.” Inji Bappah Aliyu Misau.

A nasa bangare Hon. Bakoji Bobo Dan majalisa dake wakiltar mazabar Misau a majalisar dokoki ta jihar Bauchi ya yaba ne da irin kyakykyawan jagoranci da yace Abdul Ahmed Ningi yayi wa Al’ummar sa.

“Abdul Ningi ba kadai sanato ne ba, a’a wakiline dake wakiltar Al’ummar Arewacin Najeriya, Jajirtaccenen Dan jam’iyyar PDP ne sannan Kuma yayi abubuwa da dama na gani ya kare martabar Jam’iyyar tasa”. Inji shi.

Bakoji yayi Kira ga Yayan jam’iyyar PDP da su tabbatar da sunyi duk Mai yuwuwa domin samun nasara a zabe me zuwa.

Ita kuwa shugabar Mata Hajiya Zainab A D Rufa’i ta bayyana goyon bayan sune Dari bisa dari wa Sanata Abdul Ahmed Ningi.

Tace “Abdul Ningi zai samu cikakken goyon bayan mu musamman mu Mata lura da irin kyakykyawan ayyukan cigaba da ya kawo mana a baya, zhiri min gwada shi Kuma shi na kwarai ne, muna da tabbaci yanzu zaiyi fiye da na baya.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: