Ahmed Joda Ya Rasu A Lokacin Da Nijeriya Ke Bukatar Irinsa, Inji Inuwa Yahaya
Daga Idris Shehu Zarge
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewar rasuwar Alhaji Ahmad Joda a daidai wannan lokacin wani babban rashi ne ga Nijeriya da cigabanta.
Inuwa wanda ya ziyarci Yolan Jihar Adamawa, inda ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan dattijo kuma tsohon babban sakatare a gwamnatin tarayya Alhaji Ahmed Joda, wadda ya rasu ranar Alhamis a Yola yana da shekaru 91.
Ya bayyana rasuwar ta Alhaji Ahmed Joda a matsayin babbar rashi ga kasar nan, wacce ta faru a daidai lokacin da kasar ke matukar bukatar hikimomi da shawarwarin sa.
Gwamna Inuwa wadda ya samu rakiyar Babban Daraktan Gudanarwan Kamfanin Man Fetur na Kasa NNPC Engr Mele Kyari, ya yaba wa marigayi dattijon wadda ya bayyana a matsayin dan kishin kasa, wadda ya hidimtawa Nijeriya a matakai daban-daban kuma ya bar tarihin da ba za a taba mantawa da shi ba.
Kamar yadda Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya nakalto, Gwamna Inuwa sai ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da gwamnati da al’ummar Jihar Adamawa bisa wannan babban rashi, yana mai addu’ar Allah ya gafarta masa yasa Aljannah Firdausi ce makomarsa.