Uncategorized

Ina Goyon Bayan Duk ‘Yan Takarar APC Dari Bisa Dari – Buhari

Daga Khalid Idris Doya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shaida cewar, yana tare dari bisa dari da dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar APC na zaben 2023 da ke tafe kuma na goyon bayansu dukka.

Buhari wanda ke jawabi a wajen taron kaddamar da yakin zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jihar Gombe ranar Litinin da ya gudana a filin wasanni na Stadium, ya shaida cewar, zai bada dukkanin goyon bayansa ga ‘yan takarar APC a dukkanin matakai.

Buhari wanda ke magana ta bakin ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya shure dukkanin wata jita-jitan da ke cewa baya goyon bayan wasu ‘yan takarar APC, ya ce sam babu hakan.

Buhari ya kuma kara da cewa lura da irin ayyukan da gwamnatinsa ta shimfida a jihar Gombe ya tabbatar al’ummar jihar na goyon bayansa kuma ya nemi alfarmarsu da su sake zabin APC domin ta daura daga kyawawan ayyukan da gwamnatinsa suka aiwatar.

Buhari ya ce a yi APC daga kasa har sama, ya roki al’umma da su sake bai wa APC cikakken dama.

Taron ya hada fuskokin jiga-jigan APC a ciki da wajen jihar tare da kwamitin yakin zaben Tinubu/Shettima.

Leave a Reply