Hausa

AAC Ta Samu Kujerar Kansila A Bauchi

Yunusa Muhammed na jami’yyar African Action Congress (AAC) ya lashe zaɓen kujerar Kansila ta yankin Papa ta arewa a ƙaramar hukumar Darazo inda ya kayar da babban abokin karawarsa Ashiru Muhammad na jam’iyyar PDP a yayin zaben kananan hukumomi da ke gudana a jihar Bauchi.

Yunusa Muhammad ya samu ƙuri’u 1,156, a yayin da Ashiru Muhammad daga jam’iyyar PDP ya zo na biyu da ƙuri’u 1,053 sai Idris Muhammad daga APC da ƙuri’u 290.

Leave a Reply