Hausa

Gwamna Inuwa, Ministan Sufuri Sun Ƙaddamar Da Ayyukan Asusun TETfund A GSU

 

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya jaddada aniyarsa ta haɗa kai da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETfund) don inganta ababen more rayuwa a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) da sauran manyan makarantu mallakar jihar ta yadda za a samar da yanayi mai kyau na koyarwa da koyarwa. 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin ƙaddamar da wasu ayyuka da asusun na TETfund ya gudanar a Jami’ar Jihar ta Gombe. 

Yayin da yake jaddada irin muhimmancin da jami’ar ke da shi ga al’umma, Gwamnan ya miƙa godiyarsa ga waɗanda suka taka muhimmiyar rawar da suka taka wajen kafata, Musamman tsohon Gwamna Dajuma Goje da Marigayi Farfesa Abdullahi Mahdi wanda ya kasance mataimakin shugaban jami’ar na farko, wanda ya jagoranci jami’ar har ta zama cibiyar samar da ƙwararrun da suka zama abin alfahari ga al’ummar jihar da kewaye. 

Gwamna Inuwa ya tuna da irin damar da ya samu na zama mamba a kwamitin tsare-tsare da aiwatarwa a lokacin da aka kafa jami’ar a 2004, a lokacin yana kwamishinan kuɗi. 

“A tsawon shekarun nan, mutane da dama da suka haɗa da ɗalibai da ma’aikatan da suka yi hulɗa da wannar jami’a, sun bada gudunmawa sosai ga ci gaban al’ummarmu, musamman a nan Jihar Gombe, ina mai tabbatar muku cewa da yardar Allah za mu ci gaba da bada gudumawa sosai, za mu ci gaba da jajircewa wajen ganin jami’ar ta kai wani matsayi mai girma. Za mu iya cimma hakan ne ta hanyar sadaukar da kai ga ayyukan da muke yi.” Inji shi.

Gwamnan ya ƙara da cewa, “Da zuwa na gwamna, babban abinda na fara maida hankali akai a wannar jami’a shine ɗinke gagarumin kwarin da ya tashi tun daga Jami’ar har zuwa Unguwar Malam Inna, da Anguwa Uku, lamarin da ya taimaka sosai wajen kare wannan ɗakin taro, da ɗakunan kwanan ɗalibai, da sauran gine-gine a cikin jami’ar.

Ya kuma bayyana fatan cewa, za a yi amfani da sabbin gine-ginen da aka ƙaddamar yadda ya kamata, tare da tabbatar da cewa al’umma masu zuwa sun ci gajiyarsu yadda ya kamata a jami’ar. 

Ya bayyana ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da haɗa ƙarfi da ƙarfe da Asusun TETfund don ƙara ƙara yin haɗin gwiwa yayin da manyan makarantun jihar ke ci gaba da haɓaka. 

Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga TETfund bisa yadda yake kai ɗauki a manyan makarantun jihar musamman a ƙarƙashin jagorancin Arc. Sonny Echono, mutumin da ya bayyana a matsayin gogaggen shugaba. 

Ya kuma bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a faɗaɗa Jami’ar ta Jihar Gombe zuwa reshenta na Dukku, wanda yace zai kasance tsangayar kimiyyar muhalli. 

Gwamna Inuwa ne ya ƙaddamar da tsangayar ilimi, yayin da ministan sufuri, Senaya Sa’idu Ahmed Alkali, wanda ya wakilci shugaban ƙasa Bola Tinubu, da Hon. Aishatu Jibir Dukku, da sauran manyan baƙi suka ƙaddamar da sauran tsangayu. 

Tun da farko, Babban Sakataren Asusun Tallafawa Manyan makarantun na TETfund, Arc. Sonny Echono, ya bayyana cewa tun lokacin da jami’ar Jihar Gombe ta shiga sahun jami’o’i masu cin gajiyar tallafin TETfund a shekarar 2006, ya zuwa yanzu ta samu tallafin ayyuka na fiye da naira biliyan 15, wanda ya kai kaso 86 na kuɗaɗen da ake warewa jami’ar. 

Arc. Echono ya nuna farin cikinsa da cewa, an yi amfani da kuɗaɗen da aka warewa Jami’ar yadda ya kamata, wajen samar da kayayyakin da ake buƙata a jami’ar, yana mai cewa ayyukan da asusun ya bayar sun yi tasiri matuƙa kan ayyukan da jami’ar ke gudanarwa na koyo da koyarwa da harkokin bincike. 

Ya kuma yabawa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa gudanarwar Jami’ar yadda ya kamata, ta hanyar sanya ido kan ayyukan tallafin da asusun ke aiwatarwa tun daga farko. 

A wani ɓangaren kuma, Gwamnan ya samu halartar taron haɗakar yaye ɗaliban jami’ar karo na 10, dana 11, dana 12, da kuma na 13. 

Lakcar wacce Dr. Usman Bugaje ya gabatar ta mayar da hankali ne akan taken “Ilimi da Ci Gaba: Ƙalubalen Ƙwarewa da Ɗabi’u a Jami’o’in Najeriya” 

Gwamnan ya samu rufa bayan manyan baƙi da suka haɗa da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Saminu Turaki, da tsohon shugaban asusun TETfund Alhaji Kashim Ibrahim Imam da dai sauran su.

Leave a Reply