Hausa

Akwai Bukatar Gwamnan Bauchi Ya Zurfafa Bincike Kan Dakatar Da Hakimin Burra, Inji Kungiya

Wata kungiyar cigaban matasa a Gundumar Burra da ke karamar Hukumar Ningi ta yi kira ga gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad da ya duba hukuncin dakatar da Mai girma Hakimin Burra Alhaji Ya’u Shehu Abubakar a matsayin Hakimin Burra.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnan da ya dauki matakin gaggawa domin daina rarraba gonaki da aka yi a dajin Burra Lame mallakar Jihar, wanda a yanzu aka sa kaimin kassara shi.

Jami’in watsa labarai na kungiyar Barista Muhammad Shamsuddeen Salihu, shi ne ya yi wannan kira a wani zantawarsa da manema labarai.

Salihu, wanda ya koka dacewa an dakatar da Hakimin Burra ne a kokarinsa na kare martabar dajin, wanda tun kafin rarraba dajin yake fafutukar ganin ya hana yin gawayi, da katako a yankin nasa, ya yi nuni da cewa Hakimin ya bayar da gudumawa sosai wadda ya gina, Upper Sharia Court, gina makarantun Islamiya guda uku, tare da baiwa kungiyar Izala babbar makaranta mai dauke da azuzuwa 20 inda suke islamiyya, nursery, Firamare da Higher Islam.

“Ya kuma gina Town Hall inda a yanzu aka mayar da shi gidan ‘yan-sanda, ya yi gyaran dakunan kwantar da majinyata a babban asibitin Burra gami da baiwa matasa jari domin ciresu daga harkar saran daji da shan kwaya.”

Ya shaida cewa, “Bayan takardar dakatarwa na tsahon watanni uku da mahukkuntan karamar hukuma ta aikewa Hakimin a makon da ya gabata, daga bisani Hukumar kula da kananan hukumomin jihar ta aike da takarda zuwa karamar hukumar domin dakatar da ita bisa daukar wannan mataki gami da umartarta da ta janye takardar da ta turawa hakimin, Amma ta yi biris da umarnin da aka ba ta inda tuni aka tura da wakili zuwa Gundumar.”

Kakakin kungiyar ya yi kira ga gwamnan wanda yake sauraron koken al’umarsa da ya yi watsi da duk wata jita-jita ya kafa kwamati mai adalci domin duba wannan lamari.

Da ya ke magana dangane da barna da aka yi a dajin kuwa Barista Shamsuddeen Salihu, ya ce “Duk da cewa wadanda suke da alhakin rarraba dajin sun ce daga wurin gwamna suka samu umarni, to abin a yanzu ya wuce gona da iri yadda ake kassara dajin fiye da tunani, hakan barazana ce babba domin ana baiwa Fulani ‘yan kaura wadanda ba asan daka ina suke ba da kuma wasu daga sassan jihohi kamar Kano, Kaduna, Zamafara da Katsina.”

Ya yi mamakin yadda kungiyar tayi sojan gona da sunan gwamnati ce ta sahale musu su rarraba dajin ga al’umma domin gonaki, duk da hukumomi da ma’aikata da gwamnatin take da shi a fannin muhalli da dazuka.

Barr. Salihu ya yi fatan cewa gwamnan zai duba wannan batu da idon basira domin kaso tamanin na al’umar yankin ba kaunar wannan abin da yake faruwa suke ba.

Da yake jawabi dangane da wannan batu a makon da ya gabata shugaban karamar Hukumar Ningi Hon. Mamuda Hassan Tabla, ya ce sun dakatar da Hakimin ne bisa taka haye da ya ke yiwa karamar hukumar.

A cikin ra’ayoyinsu dabam-dabam wasu daga cikin mazauna garin Burra, Auwalu Abdullahi AA, Hassan Aliyu Burra da Sakataren kungiyar Miyetti Allah na Gundumar Burra, sun yi zargin an dakatar da Hakimin ne sabida ra’ayinsa ya sha bambam da mahukuntan karamar hukumar, sun kalubalanci kungiyar da take aikin rarraba dajin da ta fito ta yi wa mutane bayani karara kan ina suke kai kudin da suke karba, sun nemi gwamnati ta binciki ababen da suke faruwa.

Sun tabbatar da cewa ana rarraba dajin Lame Burra ne idan mutum ya bayar da kudi ta hanun wata kungiyar (Hada kan Manoma da Makiyaya) ta kasar Burra karkashin shugabancin Malam Uba Ahmad, wanda har yanzu ba’asan kudin ke shiga ba.

Domin tabbatar da wannan batu manema labarai sun tuntubi shugaban kungiyar ta wayar tarho wanda ke da alhakin rarraba dajin Mal Uba Ahmad Burra, akan kudin da ake zargin suna karba, ya amsa cewar suna karbar kudi a hanun wadanda ake rabawa dajin, sai dai  baya wuce naira dubu goma zuwa ashirin.

Malam Uba Ahamed Burra ya tabbatar da cewa wannan kudi ko sisi baya shiga aljihun gwamnati  kaiwa suna amfani da shine wajen aikace-aikacen kungiyar.

Mun yi kokarin jin ta bakin jami’i mai kula da wannan daji Comrade Bello, bai dauki waya ba duk da sakonni da aka aika masa ta layin wayarsa.

A kwanakin baya ne wani kwamatin Majalisar dokokin Jihar Bauchi Kan Dazuka karkashin jagoranci Hon Wakili Nakwada, ya gana da dukkanin masu ruwa da tsaki akan wannan batu domin tabbatar da bin doka da oda.

Idan za a iya tunawa, shugaban kungiyar ‘yan jarida (NUJ) reshen Jihar Bauchi Comrade Garba Sa’idu, ya yi Allah wadai da saran Daji da ake yi a karamar Hukumar Ningi ba bisa ka’ida ba.

Shugaban ya sanar da haka ne a cikin bukukuwan makon ‘yan jarida na bana, a lokacin da suke kaddamar da dashen Bishiyoyi a jami’a mallakin jihar.

Shugaban ya yi kira ga mahukuntan karamar Hukumar da sukawar da bam bamce bam bamcen dake tsakanin su don magance matsalar duba da yadda illar hakan take da shi.

Leave a Reply