Uncategorized

Fadar Bauchi ta karrama Alh. Aliyu Aminu Garu da sarautan Sarkin Alhazan Bauchi

By Abubakar Muhammadu

Masarautar bauchi karkashin mulkin Mai martaba sarkin bauchi Alh. Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu tare da “yan Majalisan Sa Sun Nada Alhaji Aliyu Aminu Garu a matsayin SARKIN AlHAZAN BAUCHI biyo bayan la’akari da dacewar sa da kuma kyawawan halayen Sa.

Bayani na nadin sarautar nasa na kunshe ne a wata takarda da tasamu Sa Hannun Magatakardan majalisar, Alhaji Shehu Mudi Muhammad ya fitar a Ranar 27 ga watan Yulin Shekara 2022, aka rabawa manema labarai a jihar bauchi.

Takardan ta cigaba da bayyana cewa Mai Martaba Sarki da ‘yan majalisar Sa sunyi wa Sarkin Alhazan bauchi na farko, murnar samun wannan sarauta, tare da yin Kira gareshi wajan cigaba da bayar da goyan bayan sa domin cigaba da daukaka
wannan masarautar ta Bauchi.

Leave a Reply