Uncategorized

APC Ta Dage Babban Taronta Zuwa 12 Ga Maris

Daga: Mohammed kaka Misau, Bauchi.
Kwamitin riko kuma mai alhakin shirya babban taron jam’iyyar APC (CECPC) ya dage babban taron jam’iyyar na kasa (National Convention) zuwa ranar 12 ga watan Maris.

Zaben shugabannin jam’iyyar da aka ware ranar 26 ga watan Fabrairu tun da fari domin gudanar da shi ba zai gudana a wannan ranar ba. Inda aka samu Karin makonni biyu kan wannan ranar.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar wa BausheTimes cewa, Kwamitin rikon jam’iyyar da ke karkashin gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, na kan gudanar da tsare-tsarensa domin ganin an Sami nasarar gudanar da babban taron cikn nasara da kwanciyar hankali.

Leave a Reply