Buhari Ya Nada Sabon Babban Sakataren TETFund
![](https://i0.wp.com/baushetimes.com/wp-content/uploads/2022/03/download-1.jpeg?resize=289%2C173&ssl=1)
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sunday Echono a matsayin sabon babban sakataren Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund).
Nadin na Echono na kunshe ne ta cikin sanarwar da kakakin hukumar Ben Goong ya fitar a ranar Juma’a.
Echono wanda ya canji Farfesa Sulaiman Elias Bogoro daga wannan mukamin wanda wa’adin aikinsa ya kare a watan Maris.