Uncategorized

Da Dumi-Dumi: Dan Takarar APC Ya Kada Sanata Mai Ci A Bauchi Ta Kudu

Daga Khalid Idris Doya

Dan takarar Sanatan Bauchi ta Kudu, Alhaji Shehu Buba ya kayar da Sanata mai ci a halin yanzu, Sanata Lawan Yahaya Gumau na jam’iyyar NNPP a zaben Sanatan da aka gudanar a ranar Asabar.

Kazalika, Bubu ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Garba Dahiru da kuri’un da ba su da wani yawa sosai.

Da ya ke bayyana sakamakon zaben a daren ranar Litinin, baturen tattara sakamakon zaben Sanatan, Farfesa Ibrahim Hassan na jami’ar ATBU da ke Bauchi, ya bayyana cewar dan takarar APC, Shehu Buba ya samu kuri’u 170,505, inda ya kada abokin nemansa na PDP, Garba Dahiru da ya samu kuri’u 165,727.

Shi kuma Lawan Yahaya Gumau ya samu kuri’u 53,739 ne kacal da ya Sha kasa da mummunar kaye.

Leave a Reply