Uncategorized

Dabi’ar Sara suka : Mece Sila, mafita da kuma hanyar magancenta.

Daga: Habeeb Lawan Nalele

Halinda al’ummar mu ta shiga musamman ma matasan mu na Jos abune da ba’a san matasanmu da yiba, amman yanzu yazama ruwan dare a kowace Unguwa ta cikin garin Jos, Shin ta ina gizo ke sakar ne a tsskanin matasan mu ?

Abunda nakeso nayi bayani anan shine akan dabi’ar da matasan mu suka dauka na Sara Suka a kowace Unguwa, kuma ko wacce yanki da irin yadda take kiran nata wanda a baya ansan matasan mu da neman na Kansu amman yanzu yanayin ya sauya zani.

Lamura a halin yanzu sun Chanja, ta yadda a baya alokacin da muke yaranta da kuruciyar mu bamu wani waje daya wuce muje karatun Allo da makarantar dare, da wasu a cikin mu da aka sa su a makarantar Boko wasan mu ba ya wuce ran Alhamis da Jumma’a kuma wasan bai wuci na langa ko wasan turna da dai sauran wasa ba kamar Kwallo, yaran mata kuma wasan su baya wuce na gada’ da tsuniyar kizo da koqi.

Yayin da yara suka fara datawa shine zakaga Suna wasan kwallo ko zuwa dibar mangoro ko wanka a rafi shima ba dukkan yarane suke zuwa wanka a rafi ba, kuma mafi yawan yara alokacin zakasamu bayan dawowa daga makarata mafi yawa daga cikin yara za su dauki talla wasu Suna shiga gida gida, matasan kuma suna bin layi layi suna talla wasu kuma suna koyan Sana’a ,wasu tallan goro , wasu tallan sabulu mai agwagwa wasu tallan sugar mai iyali wasu har tallan abincin siyarwa ko kunun zaki da dai sauran kayan makulashe.
Kowa a cikin yara da matasan kokarinshi ace yafi abokin shi kokarin karatu ko neman na kanshi ba a wasan fada koh zuwa wajen da bai dace yara suje ba, amman yaran yanzu tun ba su wuce shekara uku ko hudu ko biyar ba, za kaga har sun san wasan banza, da abu ya tashi sai kaji yaro ya fara cewa zan sheke ka koh kaga ya dauki makami wai shi zai yi fada dashi.

A gaskiya wannan dabi’a tasamo asali ne daga irin cigaban da aka samu na hana yara lokacin yin karatu. A baya mu ranar wasan mu biyu ce a sati Alhamis da Jumma’a kamar yadda na fada a baya, sauran ranakun kuwa ba lokacin hutu amman da sannu aka fara kashe karatun makarantun dare, aka zo na Allo datalla saboda mun sake dabi’unmu da al’ada mun dauki al’adar turawa da wadanda ba al’adarmu daya da suba.

A hakikanin gaskiya iyaye da shugabanni da matasa da Yan siyasar mu dole ne a garemu mu nemawa yan ‘baya mafuta in bahaka fah toh a gaskiya zamu gaba abun zai zamo bashida kyau a garemu, domin kowace al’ummah a qasa tsayawa takeyi akan yaranta na ganin ba su lalace ba duk da suma akwai bata gari a cikin su.

Allah yabamu mafita Allah ya shirya mana zuri’armu Allah ya manana maganin wannan fitina da take yaduwa a cikin al’ummar mu.

Leave a Reply