Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Biyar: Sallar Tarawihi

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya aiko Manzanni, don su sanar da mutane Allah, su san shi da Siffofinsa da girmansa, su sanar da su hakkokinsa a kansu, don rayuwarsu ta inganta a Duniya, kuma su samu sakamako na yardar Allah da gidan Aljanna a Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Ya gabata cewa Sallar Tarawihi tana cikin Sallar daren Ramadhan, wato ita ce Sallar da mutane suka saba yi a farkon dare. Kuma an kira ta da sunan TARAWIHI ne saboda mutane suna tsawaita sallar, suna hutawa bayan duk raka’a hudu.

Ita Sallar Tarawihi Annabi (saw) ne farkon wanda ya sunnanta ta a Masallaci a cikin jam’i, sai kuma ya bari tsoron kar a farlanta ta ga al’umma, daga baya su zo su kasa yi. Ya tabbata daga A’isha (ra) ta ce: ((Wata rana da dare Manzon Allah ya yi sallah a Masallaci, sai mutane suka bi shi sallar, a rana ta gaba ma ya yi sallar, sai mutane suka yawaita, sai suka sake taruwa a a rana ta uku ko ta hudu, sai Manzon Allah (saw) bai fito ba. Da gari ya waye sai ya ce: “Hakika na ga abin da kuka yi, babu abin da ya hana ni fitowa gare ku face na ji tsoron kar a farlanta muku sallar ce”. Kuma hakan a Ramadhan ne)). Bukhari (1129) da Muslim (761).
Haka ya tabbata daga Abu Zarr (ra) ya ce: ((Mun yi Azumi tare da Manzon Allah (saw), amma bai yi mana sallar dare ba a watan har sai saura kwana bakwai watan ya fita, sai ya yi mana sallar dare har sai da daya bisa ukun dare ya tafi, sai bai yi mana sallar a saura kwana shida ba, sai ya yi mana sallar dare a rana ta biyar na karewar wata, har sai rabin dare ya tafi. Sai na ce: Ya Manzon Allah, da mun yi sallar har karshen daren. Sai Annabi (saw) ya ce: “Lallai duk wanda ya yi sallar tare da Liman har karshe to za a rubuta masa ladan tsayuwar dukkan dare”)). Abu Dawud (1375), Tirmiziy (806), Nasa’iy (1605), Ibnu Majah (1327).

Magabata sun yi sabani a kan yawan raka’o’in Sallar Tarawihi da Witri a tare da ita, wasu suka ce: raka’a arba’in da daya, wasu suka ce: raka’a talatin da tara, wasu suka ce: ishirin da tara, wasu suka ce: ishirin da uku, wasu suka ce: goma sha tara, wasu suka ce: goma sha uku wasu suka ce: goma sha daya, da sauransu. Amma abin da ya fi rinjaye shi ne goma sha daya ko sha uku, saboda abin da ya tabbata daga A’isha (ra); an tambaye ta, yaya Sallar Annabi (saw) ta kasance a Ramadhan? Sai ta ce: ((Bai kasance yana kari a kan raka’a goma sha daya ba, a Ramadhan ko waninsa)). Bukhari (2013), Muslim (738).
Haka ya tabbata daga Ibnu Abbas (ra) ya ce: ((Sallar Annabi (saw) ta kasance raka’a goma sha uku ne)), yana nufin da dare. Bukhari (1138).
Haka ya tabbata daga al-Sa’ib bn Yazeed (ra) ya ce: ((Umar (ra) ya umurci Ubayyi bn Ka’ab da Tameem al-Dariy da su yi sallah wa mutane raka’a goma sha daya)). Muwadda’ (4).

Amma su magabata sun kasance suna tsawaita raka’o’in sosai, kamar yadda al-Sa’ib bn Yazeed (ra) ya ce: ((Limamin yana karanta daruruwan Ayoyi, har mun kasance muna dogara a kan sanda saboda tsawaita tsayuwa, ba ma gamawa sai kusan al-fijr)). Muwadda’ (4).

Sabanin abin da yake faruwa a yau, ta yadda mutane suke yin Tarawihin da sauri sosai, babu nitsuwa, alhali rukuni ne a cikin sallah, wanda sallah ba ta inganta sai da shi. Kuma Malamai sun ce: Makruhi ne Liman ya yi saurin da zai hana mamu aikata Sunna a cikin Sallah, ina kuma ga saurin da zai hana su aikata wajibi?! Allah ya kyauta.

Bai kamata ga mutum ya ki halartar Sallar Tarawihi ba, ya kamata ya halarta don ya samu ladanta, kuma kar ya fita har sai Liman ya gama gaba daya, don ya samu ladan Sallar daren gaba daya.

Ya halarta mata su halarci Sallar Tarawihi a Massalaci, idan babu tsoron za a fitinu da su, saboda Annabi (saw) ya ce: ((Kar ku hana bayin Allah mata zuwa Masallatan Allah)). Bukhari (900), Muslim (442). Kuma haka aikin magabata ne, amma sai dai wajibi ne mace ta zo cikin hijabi, ba tare da bayyana ado ko tsiraici ba, ba tare da shafa turare ko daga murya ba, saboda Allah ya ce: {Kar su bayyana adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi}. [al-Nur: 31]. Ma’ana; sai dai abin da dole zai bayyana, kamar abaya da mayafi da makamancinsu. Kuma saboda Annabi (saw) ya umurci mata da su fita Sallah a ranar Eidi, Ummu Adiyya ta ce: ((Ya Manzon Allah, dayanmu ba ta da mayafi, sai ya ce: “‘Yar’uwarta ta ba ta ta saka”)). Bukhari (324), Muslim (890).

Abin da yake Sunna game da mata shi ne su zama a bayan maza, a nesa da su, su fara safu daga na karshe sai na gaba da shi…, sabanin na maza, kamar yadda Annabi (saw) ya ce: ((Mafi alherin safun maza shi ne na farko, mafi sharrinsa kuma shi ne na karshe. Mafi alherin safun mata shi ne na karshe, mafi sharrinsa kuma shi ne na farko)). Muslim (440).

Ana gama Sallah Liman yana yin Sallama ta karshe sai mata su yi sauri su tafi, bai halasta su jinkirta ba tare da uzuri ba, saboda ya tabbata Ummu Salama ta ce: ((Annabi (saw) ya kasance idan ya yi sallama mata suna tashi su tafi da zaran ya gama sallamarsa, kuma yana zama kadan kafin ya tashi ya tafi)). Ibnu Shihab ya ce: – Allahu A’alam – ina ganin hakan ya kasance ne don matan su gama fita kafin wanda ya fita cikin maza ya iso su)). Bukhari (837).

Saboda haka lallai Sallar Tarawihi abin kwadaitarwa ne matuka, saboda yin Sallah tare da Liman, har karshe ladansa shi ne ladan Sallar daren gaba dayansa.

Don haka dan’uwa kar ka yi sakaci ka yi asaran falaloli da alherai da albarka da suke cikin wannar Sallah, ka zage damtse ka lazimci yinta tare da Liman har karshe, don ka dace da gafarar Allah Madaukaki.

Allah ya karba mana, ya ba mu yalwar arziki da tsaro da zaman lafiya, ya kawo mana karshen ta’addanci da garkuwa da mutane da muke fama da su a kasarmu, ya ba mu shugabanni na gari, masu kyawawan manufofi na cigaban al’umma, tare da tausayin talakawa.

One thought on “DARUSAN RAMADHAN

Leave a Reply