Uncategorized

FIDA Na Bukatar Sakan Wa Mata Mara Kan Fasaha Da Kirkire-kirkire


Daga Khalid Idris Doya
Wata Kungiyar mata lauyoyi ta kasa ‘Federation of Women Lawyers’ (FIDA) reshen jihar Bauchi, ta nuna bukatar da ke akwai na sakan wa mata cikakken dama domin su baje baiwar fasahar da Allah ya huwace musu ta hanyar amfani da fasahar zamani, kimiyya da kuma kirkire-kirkire na fasaha.


A wata sanarwar da shugabar kungiyar reshen jihar Bauchi, Fatima Abubakar ta fitar domin raya ranar mata ta duniya na wannan shekarar mai taken Maida hankali kan gagarumin rawar da kirkire-kirkire da fasaha ke takawa wajen inganta daidaiton jinsi a tsakanin maza da mata.


FITA ta ce, lura da yadda zamani ke tafiya a halin yanzu, kirkira da fasaha su ne hanyoyi da suka fi dace a maida hankali a kai. Kana, sannu a hankali fasaha na shiga cikin harkokin rayuwa na yau da gobe, ayyukanmu, sadarwa, hada-hadar cinikayya, koyo da koyarwa da kuma sha’anin sarrafa kudade.


Kazalika, kungiyar ta nuna damuwarta kan yadda mata kalilan ke samun dama wajen baje baiwar da Allah ya musu na fasaha a wurare daban-daban.


“Mun yi la’alari da kalubalen da mata ke fuskanta a wannan fannin saboda yadda aka saba tun da farko bisa al’adar da ya dakile mata musamman iyaye.


“Fasaha ya bude sabon babi wa mata a bangaren aiki domin kuwa su na samun damar tafiyar da harkokinsu na kashin kai da kuma na ayyukansu da shi.


“Ko a lokacin annobar Korona da ya tilasta wa mata aiki daga gida. Mun jinjina wa kokarin mata ta yadda suka tashi suka koya suka kuma rungumi amfani da kimiyya da fasaha.”


FIDA ta kara da cewa, bisa rungumar kimiyya da mata suka yi, hakan ya bude musu sabbon babin koyon ilimi ta yadda suke iya amfani da shiga dauran darussan kwasa-kwasai ta hanyar yanar gizo a fadin duniya, “Hakan ya bude damarmaki sosai masu kyau da nagarta ga ‘yan uwa mata da ke taimaka mana a fannonin aikinmu sosai.”


Don haka FIDa ta ce, akwai gayar bukatar a cire dukkanin wani banbance-banbancen da ke dakile mata daga shiga a dama da su a harkar kimiyya, kungiyar tana mai cewa babu wani nau’in fasaha da wani namiji zai iya shiga a dama da shi da mata ma ba za su iya yin hakan ba.
Fatima ta karfafi mata a Nijeriya da suke shiga a dama da su a dukkanin wani gasa ko gabzatar gwajin fasaha da ake sanyawa a ko’ina a duniya domin bai wa mata cikakken dama da kwarin guiwar amfanuwa da kimiyya tare da kara samun damarmaki a fannin. Ta kuma nemi masu ruwa da tsaki da suke daukan nauyin mata wajen neman ilimi a fannin kimiyya, Fasaha da lisasafi (STEM) domin karfafa wa mata masu tasowa guiwa.


Kazalika, kungiyar ta ce akwai kuma bukatar cigaba da wayar wa yara mata alfanun da kimiyya ke da shi a garesu da cigaban al’umma.
Daga bisani kungiyar ta yi sha’awar a shawo kan banbance-banbance da ake da su a tsakanin maza da mata a fannin kimiyya da Fasaha domin Mata na suke samun cikakken damar guragwn ayyukan yi da bada nasu gudunmawar a cikin al’umma.

Leave a Reply